Jamus: Wasan Bundeslga na kara zafi
November 10, 2025
Wasannin Bundesliga na Jamus da aka gudanar a karshen mako, inda a ranar Jumma'ar da ta gabata Werder Bremen ta karbi bakuncin Wolfsburg ta kuma lallasa ta da ci biyu da daya. Bayer Leverkussen kuwa ta karbi bakuncin Heindenheim a ranar Asabar din karshen makon, ta kuma yi mata dukan kawo wuka da ci shida da nema. A karon farko karon a kakar bana kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ta kasa ta tsare a saman tebur ta gaza yin nasara a wasanta, inda ta tashi canjaras biyu da biyu a tattakin da ta yi zuwa gidan Union Berlin.
Ita ma Borussia Mönchengladbach ta yi abin kai, bayan da ta karbi bakuncin FC Köln tare da lallalasa ta da ci uku da daya. Ita kuwa takwararta Borussia Dortmund ta fadi babu nauyi, domin kuwa da kyar ta sha da kunne doki daya da daya a wasan da Hamburg ta karbi bakuncinsa. Hoffenheim ta karbi bakuncin RB Lepzig ta caskara ta da ci uku da daya, duk kuwa da cewa a mintuna tara da fara wasan Lepzig din ta fara zura kwallo. Sai dai ta yi rawar kafa har Hoffenheim ta rama ta kuma kara mata kwallaye biyu.
Sauran wasannin Turai
Kungiyar Real Madrid ta ci gaba da rike nata kambun na saman teburin LaLiga a Spaniya da maki 31. Koda yake a karshen mako ta tashi canjaras babu ci, yayin da ta yi tattaki zuwa gidan Rayo Valecano da ke matsayi na 12 a teburin kakar La Liga ta bana. A sauran wasanni da aka fafata kuwa, Atheletic Bilbao ta karbi bakuncin Oviedo ta kuma lallasa da ci daya mai ban haushi. Ita ma takwararta Atlético Madrid ta karbi bakuncin Lavente ta caskara ta da ci uku da daya, yayin da Sevilla takarbi bakuncin Osasuna ta kuma lallasa ta da ci daya mai ban haushi.
A gasar Premier League ta Ingila kuwa, kungiyar Arsenal na ci gaba da rike kambunta na saman tebur da maki 26 duk da canjaras biyu da biyu da ta yi a wasanta a gidan FC Sunderland. Haka ma an tashi wasa canjaras biyu da biyu tsakanin Manchester United da Tottenham, yayin da Chelsea ta karbi bakuncin FC Fulham ta kuma lallasa ta da ci uku da nema. Ita ma Aston Villa ta karbi bakuncin Bournmouth ta kuma caskara ta da ci hudu da nema, kamar yadda Nottingham Forest ta samu nasara da ci uku da nema a wasanta da Leeds United.
A Najeriya
To a gasar Premier Leuge ta Najeriya kuwa, kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars na ci gaba da samun koma-baya a kakar bana. Yanzu haka dai lamarin ya tabarbare mata har ta kai ana iya jera makonni ana yi mata gida da waje, ba tare da ta tabuka komai ba, abin da ya sanya kungiyar a matakin kasa a teburin gasar.
Wasan tennis
Novak Djokovic ya samu nasarar lashe kambunsa na 101 a wasan Tennis, inda ya lallasa takwaransa Lorenzo Musetti a wasan karshe na cin kofin Hellenic da ci hudu da shida da shida da uku da kuma bakwai da biyar. Wannan rashin nasara ta tarwatsa fatan Musetti na samun tikitin zuwa wasan karshe a gasar kungiyar 'Yan Wasan Tennis ta Duniya da za a gudanar a birnin Turin na Italiya, inda a hannu guda tuni takwaransa Felix Auger-Aliassime ya samu wannan dama. Mai shekaru 38 a duniya Djokovic ya kafa tarihi a gasar Tennis ta maza da kambun manyan wasanni 72, inda ya shallake Roger Federer da kambu daya.
Dan wasa ya samu ahuwa
Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi wa tsohon shararren dan wasan baseball din nan Darryl Strawberry afuwa. Trump ya yi wananna afuwa ga dan wasan na birnin New York Strawberry da ke tsare bisa laifin kin biyan haraji, tare da wasu mutane da dama. Strawberry ya kasance fitaccen dan wasa ga kungiyar New York Mets daga shekarar 1984 zuwa 1990, ciki kuwa har da wasan da suka yi nasasarar lashe gasar cin kofin duniya a 1986. Haka nan ma ya yi wasa da kungiyar Yankees, daga shekara ta 1995 zuwa 1999 tare da lashe wasannin cin kofin duniya biyu.
Tseren motoci
Shararren dan wasan tseren motoicn nan na Red Bull Max Verstappen zai fara babbar gasar tseren motoci ta Brazilian Grand Prix a ranar Lahadin da ke tafe, bayan da kungiyarsa ta gudanar da wasu sauye-sauye a motarsa da ya hadar da saka sabon inji da kuma karin albashi. Red Bull ta tababbatr da batun gyare-gyaren, a motar dan tseren da ke fatan lashe gasar a karo na biyar ya kammala a matsayi na 16 yayin neman gurbin shiga. Lando Norris da ke kan gaba a lashe gasar da ke da maki 39, ka iya yin nasara fiye da Verstappen.