Gasar kwallon kafa ta duniya na cike da cece-kuce
June 10, 2026
A karo na uku a tarihi, bayan 1970 da 1986, filin wasa na Azteca na Mexico ne ke karbar bakuncin wasan farko tsakanin Mexico da Afirka ta Kudu, daga cikin wasanni 104 da za a gudanar a kofin duniya . Wannan ya yi kama da wasan bude gasar cin kofin duniya ta 2010, ko da yake burin da FIFA ta Gianni Infantino ta sa gaba na da yawa, baya ga fadada gasar daga kasashe 32 zuwa 48.
Za a buga wasanni 78 a Amurka a birane 11, yayin da kanada da Mexico za su karbi bakuncin wasanni 13 kowacce. A karon farko, a filayen wasa 16 ne za a yi wasannin, wasu daga cikinsu na kai nisan kilomita 4,000, daga Guadalajara zuwa Vancouver, daga Los Angeles zuwa Boston.
A kusan tsawon makonni shida, ma'abota kwallon kafa za su kashe kwarkwatar idanunsu kan rawar da manyan taurari za su taka, tare da bibiyar kasashen da ba a taba gani ba kamar Cape Verde, Uzbekistan, da Curacao. Sai dai Ajentina karkashin jagorancin Lionel Messi mai shekaru 38 da ke shiga kofin duniya a karo na shida, na da burin ci gaba da rike da kofin duniya.
Manyan kasashe na cike da buri
Kungiyar kwallon kafar Faransa ta Ousmane Dembélé da ya lashe kyautar Ballon d'Or, za ta yi kokarin goge takaicin da ta ci a Doha a 2022 a wasan karshe da Ajentina. Su ma sauran manyan kasashe irin su Spain, Jamus, Brazil, Ingila, Portugal na da irin wannan babban buri.
Ko da yake kowace gasar kwallon kafa ta duniya na fuskantar cikas, amma ba kasafai ake samun matsaloli da ba su da alaka da tamaula kamar wannan ba, sakamakon yakin Gabas ta Tsakiya Sai a 'yan makonnin karshe ne aka tabbatar da cewa Iran za ta iya buga wasanninta a Los Angeles da Seattle.
Korar baki ciki har da alkalin wasa
Alkalin wasa Omar Artan na Somaliya da aka nada a matsayin mafi iya kyawun alkalanci a nahiyar Afirka a 2025, an hana shi shiga Amurka duk da cewa an ba shi biza. Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa, "yana da hulda da mutanen da ake zargi da kasancewa cikin kungiyoyin ta'addanci."
A Mexico na, tsaro ya kasance babban batu saboda barazanar da kungiyoyi da ke safarar miyagun kwayoyi ke yi bayan mutuwar madugunsu Nemesio Oseguera, lamarin da ya haifar da mummunan martani daga kungiyarsa. Don haka gwamnati ta tura jami'an tsaro 100,000 don sa ido kan wasanni 13 da za a yi a Guadalajara, Monterrey, da Mexico City.
Bukuwa shigen na Super Bowls
Ana tababa game da cikan filayen kwallon kafa saboda tsawwala farashin tikiti da aka yi, lamarin da ya haifar da fushi ma'abota kwallon kafa, wadanda suka kai FIFA kara. Shugaba Donald Trump na Amurka shi ma ya yi tsokaci, yana mai cewa ba zai iya biyan dala 1,000 ba, ko don kwallon wasan da Amurka za ta fafata da Paraguay a ranar Juma'a ba. Amma shugaban FIFA Infantino ya kare wannan farashi yana mai cewa ya dace da girmar bukata da ake da ita.
FIFA ta shirya bukukuwan bude gasar cin kofin duniya da kade-kade da raye-raye da wakoki a Mexico City, da Toronto, da Los Angeles, da kuma lokacin hutun rabin lokaci a wasan karshe na gasar cin kofin duniya, bisa gudunmawar mawaka kamar Madonna, BTS, da Shakira. Gianni Infantino ya ce bukukuwan za su yi kama da "Super Bowls a cikin makonni biyar," inda ake tsammanin cewar "mutane biliyan guda za su kalla daga akwatunan talabijin a gidajensu."