Spain kasa ce yankin kudu maso yammacin nahiyar Turai. ta na da kananan tsibirai da ke kusa da yankin arewacin nahiyar Afirka.
Ita ce kasa ta hudu mafi girma a Turai, sannan wakiliya ce ta Kungiyar Tarayyar Turai. Spain daula ce da ke da sarki da Firaminista mai cikakken iko. Al'adun Larabawa sun taka muhimmiyar rawa a wannan kasa.