A yau mataimakin shugaban Najeriya yake baiyana aniyarsa ta tsayawa takara | Labarai | DW | 25.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau mataimakin shugaban Najeriya yake baiyana aniyarsa ta tsayawa takara

Dubban jamaa ne suka hallara a wurinda mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar yake baiyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a zaben da zaa gudanar shekara mai zuwa.

Wannan aniya ta Atiku ta sake baiyana irin farraga dake jamiyar PDP dake mulki wadda ta dakatar da shi bayan wani sabani tsakaninsa da shugaba Obasanjo musamman game da shirinsa yin tazarce.

Ana san Atiku zai tsaya ne karkashin inuwar jamiyar Action Congress,wata babbar gamaiyar jamiyun adawa ciki har da wani bangare daga jamiyar PDP.