1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin dakile yaduwar makamai

Andrea Lueg/ Umaru AliyuDecember 24, 2014

Kasashe da kamfanoni masu kerawa da cinikin makamai a duniya, sun cimma wata yarjejeniya da nufin hana yaduwar makaman zuwa hannun wadanda basu dace ba.

https://p.dw.com/p/1E9l8
Hoto: imago stock&people

Daftarin yarjejeniyar an gabatar da shi ne tare da babban rinjaye gaban Majalisar Dinkin Duniya, inda ya sami goyon baya ba tare da wata muhawara mai tsawo ba. Bisa manufa kamata yayi kamfanoni da masana'antun kera makamai su baiyana adawarsu ga duk wani mataki na tauye cinikin hajojin nasu a kasuwannin duniya. To amma ba haka al'amarin ya kasance ba tsakanin kamfanonin kera makamai na Jamus. Shugaban gamayyar kamfanonin kera makamai na kasar Georg Wilhlm Adamowitsch ya nuna goyon bayansa ga yarjejeniyar inda yace:

"Muna daukar yarjejeniyar mai taken ATT, da Majalisar Dinkin duniya ta amince da ita game da cinikin makamai a matsayin yarjejeniya mai muhimmanci, wadda za ta yi jagora ga rage yaduwar cinikin makaman barkatai a duniya."

UN Vertrag Kontrolle Waffenhandel
Hoto: Timothy a. Clary/AFP/Getty Images

Yarjejeniyar ba za ta shafi kamfanonin Jamus ba

To sai dai a ra'ayinsa, yarjejeniyar da tun a ranar 24 ga watan Disamba ta fara aiki, ba za ta shafi tsarin cinikin makamai da kamfanonin Jamus suke yi ba, saboda dokokin kasar da suka shafi cinikin makamai, sun fi tsanani fiye da dokokin da ke kunshe a yarjejeniyar ta ATT.

Wannan ma shine ra'ayin dan majalisar dokokin Jamus, Jan van Aken, daya daga cikin masu sukan manufofin cinikin makaman Jamus a ketare, wanda ya ce yana da kyau ganin yadda yarjejeniyar ta ATT ta fara aiki yanzu to amma ya ce kudurorin dokar basu da tsanani.

"Kudirorin da ta kunsa ba masu wani tsanani bane, yadda ko kadan ba zasu hana ko rage cinikin makamai a duniya ba. Idan haka ne abin tambaya shine, me ya sanya nake ganin yarjejeniyar tana da kyau? Dalili shine a karon farko mun sami wani tsari da zai rika daidaita batun cinikin makamai a duniya. Ana iya amfani da misalai na dokokin Jamus domin a fadada su ga yarjejeniyar ta ATT."

Auswärtiges Amt Schild Berlin
Hoto: Fotolia/Tom-Hanisch

Yarjejeniyar ta zamo ta tarihi.

Lokacin da aka amince da wannan yarjejeniya tare da goyon baya mai yawa a Majaliar Dinkin Duniya, an kwatanta ta a matsayin mai dinbin tarihi. Sai dai masu sukanta sun yi korafin cewar bata tanadi wani hukunci ga duk kasar da ta keta sharuddanta ba. A daya hannun yarjejeniyar ta shimfidawa kasashen da suka sanya hannu kanta cewar ba a yarda su sayar da makamai ko wasu kayan yaki ga duk kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta dorawa takunkumin makamai ba. Yarjejeniyar ta kuma tanadi bincike mai tsanani idan kasar da za ta sayi makaman ta ce tana bukatar su ne saboda tabbatar da zamana lafiya ko aiyuka na jin-kai ko kare hakkin dan Adam. Dan majalisar dokokin Jamus, van Aken ya ce yana bukatar ganin an sami karin kasashe da zasu sanya hannu kan yarjejeniyar ta ATT. Ya zuwa yanzu kasashe 57 ne suka sanya hannu kanta, cikinsu har da Jamus, amma biyu daga cikin kasashen da suka fi cinikin makamai a duniya, wato China da Rasha basu amince da ita ba tukuna.