´Yar Aduwa ya koma gida bayan kwantar da shi a wani asibiti dake Jamus | Labarai | DW | 10.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yar Aduwa ya koma gida bayan kwantar da shi a wani asibiti dake Jamus

Bayan ya shafe kwanaki 4 ana duba lafiyar sa a wani asibiti dake nan Jamus dazu-dazun nan dan takarar shugabancin Nigeriya karkashin inuwar jam´iyar PDP kuma gwamnan jihar Katsina, Alh. Umar Shehu ´Yar Aduwa ya sauka a birnin Legas. A wani taron manema labarai da ya yi jim kadan bayan isar sa a filin saukar jiragen sama na Murtala Mohammad dake unguwar Ikeja, Alhaji ´Yar Aduwa ya godewa Ubangiji da kuma ´yan Nijeriya ga baki daya.

“Da farko ina godewa shugaban kasa da dukkan shugabanin jam´iyar PDP da dukkan magoya bayan mu da sauran ´ya´yan PDP da kuma dukkan ´yan Nigeriya da suka yi min fatan alheri.”

Yanzu haka dai Alh.´Yar Aduwa ya zarce jihar Ekiti inda zai ci-gaba da yakin neman zabe. A ranar talata da daddare aka garzaya da shi wani asibiti dake birnin Mainz na nan Jamus don duba lafiyarsa bayan yayi fama da mura.