A shekarar 1951 ce aka haifi Umaru Musa 'Yar Aduwa. Ya rike mukamin gwamnan jiharsa ta Katsina tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.
Bayan da ya kammala wa'adinsa na biyu a kan kujerar gwamna an zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekarar 2007 kuma ya rasu ne a kan kujerar a 2010 gabannin gama wa'adin mulkinsa.