Turkiyya: Zabe ya bar baya da kura | Zamantakewa | DW | 17.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Turkiyya: Zabe ya bar baya da kura

Kungiyoyi da kasashen duniya na jan hankalin kasar Turkiyya da ta yi taka tsantsan da alamun samun matsala sakamakon zaben kasar. An bayyana shugaba Erdogan a matsayin zakaran zaben raba gardama mai kuma gardandami.

Gwamnatin Jamus ta ce sakamakon zaben raba gardamar da zai baiwa shugaba Rajap Tayyib Erdogan damar fadada karfin iko da yake da shi, wani nauyi ne a kan shi a kasar da alamu ke nuna cewa ta rabu.

Shugabar gwamnati Angela Merkel da ministan harkokin waje Sigmar Gabriel, sun bayyana bukatar maganta matsalolin da kwararrun masana shari'ar nahiyar Turai suka nuna dangane da zaben raba gardamar kasar na jiya Lahadi.

Shugaba Erdogan dai ya yi nasara ne da kashi 51.3 cikin dari, yayin da wadanda suka ki amincewa sauya tsarin mulkin ke da kashi 48.7. Sai dai jam'iyyun adawa sun yi kiran a soke zaben.

Masu sa ido kan zabe na kasa da kasa ma dai sun aibanta zaben da suka ce da kura-kurai. Hukumar tarayyar Turai da shugaba Francois Hollande na Faransa, duk sun yi kiran Turkiyyar da ta gudanar da taron hadin kan kasa, saboda karancin tazarar da aka samu a zaben.

 

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin