Turkiya ta kama hanyar sauya tsarin mulki | Labarai | DW | 16.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta kama hanyar sauya tsarin mulki

Gabanin bayyana sakamakon zabe akwai yuwuwar masu neman sauya kundin tsarin mulkin Turkiya sun yi nasara a zaben raba gardama.

A kasar Turkiya rahotanne na cewa Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya samu nasarar a kuri'ar raba gardama na sauya kundin tsarin mulkin kasar. Kamfanin  dillacin labaran kasar ANADOLU ya bayyanan cewa wadanda ke son sauyin sun yi rinjaye dan karamin rata. Bayan kammala kirga kuri'u da kashi 90 cikin dari na kuri'un da aka kada, wadanda suka amince na da kashi 51, yayin da masu adawa suka samu kashi 41.

Kawo yanzu dai ba samu bayanin sakamakon a hukumance ba, kuma ba a kammala kirga kuri'u ba. Sai dai masu bin diddigin kuri'ar jin ra'ayin na cewa idan an kawo sakamakon zaben da ya gudana a kasashen waje musamman Turai to tana iya yuwuwa wadanda suka amince su kara samun rinjaye. Dama dai Shugaba Racip Tayyip Erdogan ya nemi a yi kuri'a ne domin sauya kundin tsarin mulki inda za a bai wa shugaban kasa cikakken iko, sabanin a yanzu tsarin firaminista ake bi, inda shugaba ke da mukamin jeka na yi ka.

Tuni dai man'yan jam'iyyun adawa suka yi ikirarin kin amincewa da sakamkon zaben raba gardaman, inda suka ce za su nemi kotu ta tilasta a sake kirga kuri'un.