Matanin Amirka ga Turkiyya | Labarai | DW | 18.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matanin Amirka ga Turkiyya

Shugaba Donald Trump ya taya shugaba Raccep Tayyip Erdogan murnar cin nasara a zaben da ya fadada karfinsa na iko.

Shugaba Donald Trump na Amirka ya taya shugaban Turkiyya Rajap Tayyip Erdogan murna, sakamakon nasarar da ya samu a zaben raba gardamar kasar da ya fadada karfinsa na iko. Shugaba Trump ya yi magana ne ta wayar tarho da takwaran na shi na Turkiyya Erdogan, sun kuma tattauna kan kasar Syria da kuma bukatar hada kai don yaki da ta'addanci, musamman kungiyar IS.

Ma'aikatar harkokin wajen Amirkar ta bukaci Turkiyya da ta martaba yarjeniyoyin cikin gida da na kasashen ketare da ke kanta.

Bangarorin biyu sun kuma amince da bukatar bincika shugaba Bashar Al Asad na Syria. Sun kuma amince da kulla kyakkyawar alaka tsakaninsu musamman a bangaren demokuradiyya da 'yancin fadar albarkacin baki. Amirkar ta kuma amince da rahoton masu sa ido kan zaben na Turkiyya, da suka ce an sami kura-kurai