1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar Hukumar Majalisar Dinkin Dunia mai yaki da yaduwar makaman nuklia ta kai ziyara a Iran

November 2, 2005
https://p.dw.com/p/BvMk

Kasar Iran ta gayyaci hukumar majalisar Dinkin Dunia mai yaki da yaduwar makaman nuklea ta ziyarci tashar ta sarrafan uranium da ke Parchine.

Wannan tasha na samun matukar suka daga kurraru ta fannin makaman Nuklia, tare da zargin Iran, da kera makaman kare dangi a cikin ta.

Mataimakin shugaban hukumar ta Majalisar Dinkin Dunia tare da tawagar sa, tunni su issa tashar, inda su ka fara aikin binciken.

A halin da a ke ciki kasar ta Iran, na fuskantar barazana daga kasashen turai, da Amurika na gurfanar da ita ,gaban komitin sujhu na Majalisar Dinkin dunia, a game, da taurin kai, da hukumomin kasar su ka nuna na, bada kin hadin kai ga masu binciken makaman nuklia na Majalisar Dinkin Dunia.