1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓe a jihohi biyu na Jamus.

March 27, 2011

Jam´iyar "the Greens" ta yi nasara a yayin da CDU ta Angela Merkel ta sha kaye a zaɓɓuɓukan jihohin Baden Württemberg da Rheinland Palatinate.

https://p.dw.com/p/10iKi
A.Merkel ta sha kayiHoto: AP

Jam'iyin CDU da kuma FDP da ke riƙe da madafun ikon tarayyar Jamus sun kama hanyar shan kaye a zaɓen da aka gudanar a yau ɗin nan a jihohi biyu na ƙasar. Bisa ga ƙididdigar jin ra'ayin jama´a da wata tashar talbajin ta Jamus ta gudanar tsakanin waɗanda suka kaɗa ƙuri'unsu, jam'iyar the Greens da kuma ta 'yan Social Demokrat wato SPD, sun sami jimmilar kashi 48 da ɗigo biyar daga cikin 100 na Ƙuri'un da aka kaɗa a jihar Bade Wurttenberg . yayin da jam'iyun CDU ta Angela Merkel da kuma FDP ta ministan harkokin waje Guido Westerwelle suka tashi da kashi 43 daga cikin 100. Ana ganin cewa matsayin da gwamnatin Merkel ta ɗauka game da makamashin nukilya, da kuma matsalar koma baya tattalin arziki na duniya da ya shafi Jamus da kuma matsayinta game da rikicin Libya na daga cikin dalilan da suka haifar mata da wannan koma bayan. A jihar Rheinland Palatinate ma, jam´iyar the Greens da kuma SPD sun sami jimmilar ƙuri'u da yawansu zai iya basu damar kafa gwamnati ta gaba. 'yayin da gwamnan wannan jiha da ya shafe shekaru 16 akan karaga ya tashi da kashi 35 daga cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Yahouza Sadissou Madobi