1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta ci gaba da kare manufofinta

November 6, 2014

Tsohon shugaban kasar Rasha a karkashin Tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev ya ce zai ci gaba da kare manufofin Shugaba Vladimir Putin.

https://p.dw.com/p/1DiMP
Hoto: AP

Mikhail Gorbachev ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke tattaunawa da kafar yada labarai ta Interfax, inda ya ce zai kare manufofin Putin din da ya bayyana a matsayin gwarzon da ke kare kasarsu a yayin tattaunawarsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel in ya halarci bukukuwan tunawa da faduwar bangon Berlin da ya yi sandiyyar sake hadewar Jamus a matsayin kasa guda shekaru 25 din da suka gabata da za a gudanar a karshen mako. Mai shekaru 83 a duniya Gorbachev ya taka muhimmiyar rawa wajen faduwar bangon na Berlin da ya yi sanadiyyar sake hadewar Jamus a matsayin kasa dunkulalliya, kuma zai halarci bikin na Berlin ne a dai-dai lokacin da ake zaman doya da manja tsakanin Rasha da kasashen yamma bisa zargin mahukuntan Moscow da su ke yi da hannu a rikicin Ukraine, zargin da Rashan ke musantawa tana mai cewa tana kare muradunta ne kawai a yankin gabashin kasar. Takaddamar da ke tsakanin bangarorin biyu dai ta sanya kasashen na yamma kakabawa Rasha takunkumi, inda ake bayyana halin da suke ciki a matsayin mafi wahala tun bayan kammala yakin cacar baka.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman.