Rasha ta gargadi Ukraine kan magoya bayanta | Labarai | DW | 23.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta gargadi Ukraine kan magoya bayanta

Rasha ta aikewa da Ukraine sako da kakkausar murya cewar za ta maida martani in Kiev ta farwa 'yan awaren da ke goyan bayan Moscow a gabashin Ukraine din.

Por-russische Separatisten in der Ostukraine

Magoya bayan Rasha da suka kame wani ginin gwamnatin Ukraine

Ministan harkokin wajen Rashan Sergie Lavrov ne ya aike da wannan sako, inda ya kara da cewar muddin aka taba mutanensu kamar yadda aka taba yi a kudancin Ossetia da ke kasar Georgia a shekara ta 2008, to Moscow za ta kasance ba ta da wani zabi illa ta maida martani kamar yadda dokokin kasa da kasa suka gindaya.

Wannan kalaman na Moscow dai na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban rikon kwaryar Ukraine Oleksandr Turchynov ya bada umarnin afkawa masu tada kayar baya a gabashin kasar bayan da aka gano wasu gawawwaki biyu ciki kuwa har da ta wani dan siyasa na jam'iyyar ta shugaban kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal