Rasha: Gargadin kasashen Yamma kan Ukraine | BATUTUWA | DW | 26.01.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Rasha: Gargadin kasashen Yamma kan Ukraine

Rasha na ci gaba da fuskantart barazanar ladabtarwa daga kasashen Turai da Amirka, bisa zargin ta da kokarin mamaye kasar Ukraine. Sai dai har yanzu kasashen EU na fama da sabanin ra'ayi.

Rasha | Atisayen sojojin Rasha

Kawo yanzu dai, Rasha ta jibge sojoji kimainin dubu 100 a kan iyakrat da Ukraine

Gargadin kasashen Yamma na kara fitowa fili, dangane da yiwuwar amfani da karfi daga Rasha wajen mamaye makwabciyarta Ukraine. A halin yanzu dai Rasha ta jibge dakaru dubu 100 a kan iyakarta da Ukraine yayin da kungiyar tsaro ta NATO ta aika da jiragen ruwa da jiragen yaki zuwa gabashin Turai, lamarin da ya saba wa bukatun fadar Kremlin kai tsaye. Sai dai babu matsaya daga nahiyar Turai kan matakin da za ta dauka, idan sojojin Rasha suka keta iyaka kuma suka mamaye Ukraine. Hasali ma a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar bayan taron da suka gudanar, ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU, sun bayyana cewa "duk wani harin soji da Rasha za ta kai wa Ukraine zai haifar da mummunan sakamako." 

Karin Bayani:  An tashi ba matsaya a taron Rasha da NATO

Sai dai a lokacin da ya gana da shugaban gwamnatin Jamus yayin ziyarar aiki da ya kawo birnin Berlin, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kiran da a ci gaba da tattaunawa da Rasha domin samar da maslaha: "A halin da ake ciki muna goyon bayan Ukraine, kuma muna ba ta cikakken hadin kai. Abu mai muhimmanci wanda shugaban gwamnatin Jamus ya yi tsoka ci a kai shi ne, ka da mu katse tattaunawa da Rasha. Kun san cewa a ko da yaushe Faransa na karfafa musayar yawu. Akwai wata muhimmiyar tattaunawa tsakanin Amirka da Rasha, yana da kyau a ci gaba da gudanar da ita. Akwai kuma tattaunawa tsakanin mu da Rasha, sannan akwai tattaunawa da OSCE."

Berlin I Tattaunawar shugaban gwamnmati Scholz da Macron

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz

Mambobin kungiyar Tarayyar Turai dai, sun dade suna gargadi game da takalar fada da Rasha ke yi wa Ukraine. Shugabannin kasashe da na gwamnatocin na Turai sun amince a tsakiyar watan Disamba da matakan ladabtarwa kan Rasha, amma kuma a daya hannu sun samu rabuwar kawuna kan abin da za su yi wa fadar mulki ta Kremlin a zahiri idan ta yi kunnen kashi. Wannan dai ba ya rasa nasaba da alakar tattalin arzikin da Rasha ke da shi da wasu daga cikin kasashen na EU, ciki har da Jamus da Ostireliya da Hangari. Da ma sanin kowa ne cewa kungiyar Tarayyar Turai na bukatar samun hadin kan duk mambobinta, domin aiwatar da duk wani mataki na siyasa. Jami'an diflomasiyya na kungiyar Tarayyar Turai ne suka sanya takunkumai ko matakan da za a dauka a kan Rasha, amma suka ce za a iya aiwatar da su ne sa'o'i 48 bayan Rasha ta mamaye Ukraine.

Karin Bayani: Har yanzu da sauran aiki gaba bayan taron Minsk

Akwai kuma bukatar samun hadin kan kasashen Amirka da Birtaniya, wadanda su ma ba su fito fili sun bayyana matakin da za su dauka ba. Ya zuwa yanzu dai babu tabbas kan takunkumin zai shafi tsarin biyan kudi na duniya wato SWIFT, ko kuma kawo karshen bututun iskar gas tsakanin Rasha da Jamus wato Nord Stream two. A nasa bangaren kuwa, ministan harkokin kasashen waje na Rashan Sergey Lavrov ya yi karin haske kan barazanar da Moscow ta ke ganin kasashen yamma na yi mata: "Amirka da kawayenta na Turai wadanda suka yi watsi da diflomasiyya, suna kokarin dakile kasarmu. Baya ga haramtaccen takunkumi na bai daya, suna kara matsin lamba na soja da ma na siyasa a kan kasar Rasha. Ku kalli atisayen sojoji da suke yi a kusa da kan iyakokinmu, inda suke jawo gwamnatin Kiev a cikin NATO, suna ba ta makamai masu guba domin tsokanar Rasha da fada."

Rasha Moscow | Taron manema labarai na ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock da takwaranta na Rasha Sergej Lawrow

Ministan harkokin kasashen wajen Rasha Sergey Lavrov

A halin yanzu muhawarar da ake yi a cibiyar Tarayyar Turai da ke a Brussels, ita ce ta bukatar fayyace ayoyin tambayoyi da ake kafawa game da inda alkiblar EU za ta dosa. Za ta kai harin soja ne idan sojojin Rasha suka tsallaka iyakar Ukraine? Mai za ta yi game da karuwar fada a gabashin Ukraine wato Crimea, inda 'yan aware suka samu damar rike yankuna tun shekara ta 2014 sakamakon goyon bayan Rasha? Kuma me za a yi idan aka kai hari ta Internet a kan muhimman ababen more rayuwa na Ukraine? Irin wadannan batutuwa dai har yanzu babu bayanai a kansu. Rasha ta bukaci kungiyar NATO ta janye sojojinta daga gabashin Turai, sannan tana son tabbacin Ukraine da Jojiya ba za su taba zama mambobin kungiyar ba kafin ta janye sojojinta daga kan iyaka da Ukraine. Sai dai NATO ta nanata cewa ba za ta sauya manufarta ta barin kofa a bude ga duk mai son zama mamba ba. Ko da yake Ukraine na son shiga kungiyar ta NATO, amma a yanzu ita ba mamba ba ce saboda haka ba za ta iya samun cikakkiyar kariyar NATO din ba.

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin