Shekara guda da zaben raba gardama a Krimiya | Siyasa | DW | 16.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekara guda da zaben raba gardama a Krimiya

Al'ummar yankin tsibirin Krimiya, sun kasance cikin murnar tunawa da zagayowar cikon shekara guda da zaben raba gardamar da ya basu damar komawa ga Rasha.

Al'ummar Krimiya na murna

Al'ummar Krimiya na murna

A wannan Litinin dai aka shirya wani babban fareti na motoci a titunan birnin Sebastopol, tare da kade-kade da raye-raye na nuna murnar duk kuwa da cecekucen da zaben ya janyo wanda ma kasashen yamma suka kira shi da haramtacce. A ranar 16 ga watan Maris na 2014 ne dai a karkashin kulawar dakaru na musamman wadanda suka mamaye mahimman wurare na wannan tsibiri na Krimiya makonni biyu kafin lokacin zaben wanda hakan ya baiwa al'ummar wadda mafi yawansu 'yan asalin kasar ta Rasha ne damar kada kuri'unsu na amincewa ga komawa ga bengaran Rasha, inda hukumomin na Krimiya suka sanar cewa a kalla an samu kashi 97 cikin 100 na wadanda suka kada kuri'ar amincewa da wannan aniya tasu. Sai dai ganin cewa an yi zaben ne ba tare da halartar wasu 'yan kallo na kasashen waje ba, ya sanya hukumomin Ukraine da ma na kasashen yamma suka kira shi a matsayi jeka na yi ka.

Tarayyar Turai na ci gaba da nuna adawa kan matakin.

Ana iya cewa, shekara guda dai bayan wannan zabe na raba gardama a yankin Krimiya, kungiyar Tarayyar Turai ta ci gaba da kafe wa kan bakanta na neman kare mutunci da hadin kan kasar Ukraine a matsayin kasa daya dunkulalliya kamar yadda shugabar Diflomasiyar ta Tarayyar Turai Federica Moghereni ta rubuta cikin wata sanarwa. Duk kuwa da takunkummin da kasashen yamma suka kakabawa Rasha, hakan bai hana shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin saka hannun kan kudirin dawowar yankin na Krimiya zuwa Rasha abun da ya haddasa fushin hukumomin na Ukraine, da ma na kasashen Yamma.

Yankin Donbass na yin koyi da Krimiya.

Oleg Zarjow da Anna Netrebko

Oleg Zarjow da Anna Netrebko

Wannan mataki da yankin na Kirimiya ya dauka na komawa ga Rasha, ya baiwa yankin Donbass mai arzikin mu'adanai da ke gabashin kasar ta Ukraine kwadayin ballewa daga Ukraine domin samun cin gashin kansu, abun da ya janyo yake-yaken da kawo yanzu ya yi sanadiyar rasuwar mutane fiye da 6000. Cikin wata sanarwa da ya fitar albarkacin zagoyowar cikon shekara guda da zaben rabagarmar shugaban majalisar dokokin yankin na Krimiya Vladimir Konstantinov ya ce, tare da Rasha suna nan suna gina sabuwar Krimiya, yayin daga nashi bengare Firaministan yankin na Krimiya Serguei Axionov ya ce idan da Krimiya ba ta koma ga Rasha ba, to da yanzu ita ma tana fuskantar matsalolin yaki kamar yadda yankin gabashin kasar ta Ukraine ke fuskanta, inda ya ce yanzu kuma tare da Rasha suna cikin kwanciyar hankali.

Sauti da bidiyo akan labarin