1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu matsaya a taron Rasha da NATO

January 13, 2022

An gaza cimma matsaya a kan kasar Ukraine, tsakanin kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN da kasar Rasha. Akwai dai kasadar yaki tsakanin bangarorin biyu, koda yake NATO ta ce za ta ci gaba da tattaunawa.

https://p.dw.com/p/45U5v
Tattaunawar NATO da Rasha a Brussels
An tashi ba tare da cimma matsaya ba a taron Rasha da NATOHoto: Alexey Vitvitsky/Sputnik/picture alliance/dpa

Mahukuntan Rasha dai, na zargin kungiyar kasashen Yammacin Duniya kan abin da ke faruwa. Tattaunawar tsakanin kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN da Rasha dai ba ta kasance da sauki ba, inda mambobin kasashe 30 suka mayar da hankali kan kasar Ukraine yayin zama da Rasha na kimanin sa'o'i hudu. Sai dai duk da tattaunawar babu abin da ya sauya, mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Rasha da ya jagorancin wakilan kasarsa Alexender Grushko ya zargi NATO da nuna cewa tana shirye wajen kawo karshen zaman tankiya tsakanin bangaorin, amma ba a ganin hakan a aikace. Tun da farko kungiyar ta NATO ta nemi Rasha ta janye dakarunta kimanin dubu 100 daga iyaka da Ukraine, sai dai har kawo yanzu Rasha ta tsaya kai da fata sai an yi mata alkawarin Ukraine ba za ta zama mamba ba a kungiyar ba tukuna. Sai dai Jens Stoltenberg babban sakataren kungiyar tsaron ta NATO ya ce Rasha ba ta da iko kan matakin mahukuntan Ukraine, idan suna bukatar shiga cikin NATO.

Dakarun sojojin Jamus da na Holland a Rukla, Lithuania
Dakarun kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN na shirin daukar mataki a kan RashaHoto: Carsten Hoffmann/dpa/picture alliance

Ana ta bangaren Wendy Sherman karamar sakatariyar harkokin wajen Amirka wadda ta jagoranci wakilan kasarta a taron tsakanin kungiyar tsaron NATO da Rasha, ta jaddada matsayin kasashen Yammacin Duniya na daukar mataki a kan Rasha muddin ta sake yin kuskuren kuste a kasar Ukaine. Amirka da kasashen kungiyar Tarayyar Turai da masu dasawa da su, na shirin kakabawa Rasha gagarumin takunkumin karya tattalin arziki, muddin ta sake kutsawa Ukraine. Sai dai jagoran wakilan na Moscow, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Alexender Grushko ya ce duk da mabambantan ra'ayoyi taron yana da amfani. A hannun guda kuma, Stoltenberg babban sakatare kungiyar NATO ya ce dole Rasha ta kasance cikin sanin abin da zai biyo baya kan kutse a Ukraine. Tun bayan zaben raba-gardama da aka yi a yankin Kirimiya na Ukraine a shekara ta 2014 da Rasha ta mamaye yankin Kirimiya na Ukranine, har yanzu ana samun karya yarjejeniyar tsagaita wuta a gabashin kasar ta Ukraine da ke fuskantar tashe-tashen hankula tsakanin dakarun Ukraine da 'yan aware masu goyon bayan Rasha.