1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara akan baki a Jamus

June 23, 2005

Ko da yake an samu ci gaba dangane da makomar zaman baki a nan Jamus amma har yau da sauran rina a kaba dangane da kyautata zaman cude-ni-in-cude-ka tsakaninsu da Jamusawa

https://p.dw.com/p/Bvb9
Marie-Luise Beck, wakiliyar gwamnati akan al'amuran baki
Marie-Luise Beck, wakiliyar gwamnati akan al'amuran bakiHoto: Presse

A lokacin da take gabatar da rahoton shekara akan halin da baki ke ciki a nan Jamus, Marie-Luise Beck, wakiliyar gwamnati akan al’amuran baki tayi kira da a kara karfafa matakan kyautata zaman cude-ni-in-cude-ka tsakanin bakin da takwarorinsu Jamusawa, musamman ta la’akari da gaskiyar cewar kimanin mutane miliyan goma sha hudu dake nan kasar suna tushe daga ketare. Ta ce a sakamakon auratayya tsakanin Jamusawa da baki ake dada samun kusantar alaka tsakanin sassan biyu, inda a yanzu zakatarar da yawa daga Jamusawan suna da dangi Rashawa ko Turkawa da makamantansu. Kimanin kashi daya bisa hudu na yaran da ake haifa a nan Jamus yanzu haka, zaka tarar daya daga cikin iyayensa dan kasar waje ne. A cikin rahoton nata Marie-Luise Beck ta ce wajibi ne a kara kyautata manufofin ilimi ga wadannan tsattsan baki. Ta ce babu wata kasa mai ci gaban masana’antu, inda damar samun ci gaba ta fuskar ilimi ta danganta da asalin mutum kamar Jamus. Wannan maganar ta shafi ‚ya’yan baki, kuma adadin nasu sai dada karuwa yake yi. A yayinda kimanin kashi daya bisa hudu na dalibai Jamusawa kann kammala makarantar sakandare, duka-duka kashi daya bisa goma ne na ‚ya’yan bakin ke samun irin wannan dama. Kimanin kashi 20% daga cikinsu ma su kann tashi ne a tutar babu. Daya daga cikin dalilan haka shi ne gibin da suke fama da shi a harshen Jamusanci. Wani abin da zai taimaka a cike wannan gibi kuwa shi ne gabatar musu da darrusan koyan Jamusanci a makarantu na gaba da faramare. Rahoton mai shafuna 600 yayi nuni da yadda matsalar rashin aikin yi tayi tsamari tsakanin baki a nan kasar, inda adadin nasu ya ribanya na Jamusawa har sau biyu. Sai dai kuma wani abin madalla shi ne kasancewar ana samun bakin a kusan dukkan bangare na harkokin yau da kullum, kama daga ‚yan kodago zuwa ga malaman makaranta da jami’o’i da hamshakan ‚yan kasuwa. Dangane da korafin da ake yi na mayar da kansu da kansu saniyar ware da bakin ke yi a wasu unguwanni, inda zaka tarar da su suna zama su ya su, Marie-Luise Beck ta ce a hakika bata da tabbatattun alkaluma game da haka, illa bin diddigin lamarin da tayi, inda ta ce akwai wasu unguwannin dake fama da matsaloli iri dabam-dabam, musamman a harkokin rayuwa ta yau da kullum. Misali ta ce akwai wata unguwa a birnin Bremmen, inda kimanin kashi 40% daga cikinsu tsattsan Jamusawa ne da suka yiwo kaura zuwa kasar baya-bayan nan, sai kuma kashi 30% na Jamusawa dake dogaro akan tallafi na gwamnati, kana ragowar kashi 30% kuma suka hada da sauran jinsunan baki daga sassa dabam-dabam na duniya. A wannan unguwar ana fama da dimbim marasa aikin yi. Amma hatta su kansu bakin da suka samu nasarar kyautata makomar rayuwarsu suka kaurace wa ire-iren wadannan unguwanni. Wani muhimmin abu a wannan bangaren shi ne a dakatar da wariyar jinsin da ake nuna wa baki wajen neman gidajen haya. Domin hakan na daya daga cikin abubuwan dake taimakawa ake samun cunkoson bakin a wasu kebnabbun unguwanni, in ji Marie-Luise Beck, wakiliyar gwamnatin Jamus akan al’amuran baki a cikin rahotonta na shekara.