Pompeo na ziyara a Jamus | Labarai | DW | 31.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pompeo na ziyara a Jamus

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo zai gana ta tokwaransa na Jamus Heiko Maas a birnin Berlin da kuma Shugabar gwamnati Angela Merkel daga bisani ya zarce zuwa kasashen Switzerland da Birtaniya.

Ziyarar Pompeo na da zimmar ganawa da shugabannin kungiyar Tarayyar Turai kan nuna matsayar Amirka ba ta neman yaki da kasar Iran. Tun a farkon watan Mayu aka Mr. Pompeo ya shirya ziyartar nahiyar Turai amma ya katse zuwa Irak cikin gaggawa domin shawo kan rikicin da ke shirin barkewa tsakanin Iran da Amirka.

Jamus na cikin kasashen Turai da ke zargin Shugaba Trump da neman haddasa yakin cacar baka da Iran ta hanyar sa mata takunkumin kasuwanci bayan da Amirka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.

A baya dai an sha kai ruwa rana tsakanin Shugaba Donald Trump da Angela Merkel kan batutuwan da suka shafi karbar bakin haure da kasuwanci da batun shinfida bututan gas daga Rasha har ma da batun kashe kudade kan tsaro.