Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Trump hamshakin dan kasuwa ne, kana dan siyasa a Amirka kuma wakili ne na jam'iyyar Republicans.
Ya na daya daga cikin 'yan Republicans da suka nemi jam'iyyar ta tsayar da su takarar zaben shugaban kasa na 2016.
Donald Trump zai zama tsohon shugaban Amirka na farko a tarihi da aka taba tuhuma da bayar da toshiyar baki don boye alaka da wata mata mai fim din batsa.
Hukumomi a amirka sun ce sun gano wasu muhimman takardun da ke kunshe da bayanan sirrin gwamnati a gidan Shugaba Joe Biden na kasar.
A kasar ta Amirka, a wannan zaben ne ake zaben dukkan 'yan majalisar wakilai, da kashi daya bisa uku na majalisar dattawa da kuma wasu mukaman shugabancin jihohi da dama.
Ana dab da zaben tsakiyar wa'adi a Amirka, zaben da ke gwaji ga kimar gwamnati mai ci. A 2014 ta tabbata cewa fitowar masu kada kuri'a ya yi kasa da kashi 42 cikin 100.
Trump, wanda ke son sake tsayawa takara a 2024, na kokarin ganin 'yan majalisar Republican 10 da suka goyi bayan zarginsa da hannu a kutsen majalisa, ba su sami tikitin jam'iyyar a zaben 'yan majalisa na Nuwamba ba.
A cikin shirin akwai labarai da rahotanni daga bangarori dabam-dabam na duniya.
Wasu majiyoyi a Amirka na cewa kotu ce ta sahale wa FBI din kutsawa gidan Donald Trump domin binciken ko ya boye wasu takardun sirri na gwamnati.
Wasu majiyoyi a Amirka na cewa kotu ce ta sahale wa FBI din kutsawa gidan Donald Trump domin bincike ko ya boye wasu takardun sirri na gwamnati.
Wasu jihohin Amirka sun sanar da fara daukar matakan hana zubar da ciki don radin kai, sakamakon hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na soke 'yancin zubar da ciki.
Tsohon shugaban kasar Amirka Donald Trump ya kaddamar da sabon shafinsa na sada zumunta, wanda ya yi wa lakabi da "Truth Social" tare da samar da shi a kan manhajar nan ta Apple's App store.
Bayan samun kuri'u masu dimbin yawa da tabbatar da Joe Biden a matsayin shugaban kasar Amirka, farin jinin shugaban ya ragu a cikin shekara guda da hawansa mulkin.
Kotun kolin Amirka ta yi watsi da bukatar tsohon Shugaban kasar Donald Trump na hana fitar da bayanan fadar White House da kwamitin majalisar dokokin kasar ya nema a harin da aka kai zauren majalisar kasar ranar 6 ga watan Janairun 2021.
Batun mika mulki cikin ruwan sanyi a Amirka na da matsayi a tsarin kasar da duniya ke koyi. Sai dai yamustin da magoya tsohon Shugaban Amirka Domald Trump suka yi a majalisar dokoki a ranar 6 ga watan Janairun bara.
Yamutsin da magoya bayan tsohon Shugaban Amirka Domald Trump suka yi abu ne da ya matukar girgiza dimukuradiyyar kasar.
Watanni 19 bayan da Amurka ta rufe iyakokinta da Kanada da Mexiko don yaki da annobar corona, gwamnatin kasar ta sake sanar da bude kofofinta ga wadanda suka yi allurar rigakafin corona.
Tun bayan da Angela Merkel ta zama shugabar gwamnatin Jamus shekaru sama 15 baya, ta yi zamani da shugabannin Amirka uku. Bayan tsamin danganta da mulkin Trump an ga canji a zamanin Joe Biden.