1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tuhumi Donald Trump kan sakaci da bayanan sirrin gwamnati

June 9, 2023

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya ce an yi kuskure a tuhumar da ake yi masa na sakaci da wasu muhimman takardun da ke dauke da bayanan sirrin gwamnati.

https://p.dw.com/p/4SMXy
Donald Trump
Hoto: Charlie Neibergall/AP/picture alliance

Stohon shugaban Amikra Donald Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewar an gayyace shi da ya bayyana a kotun birnin Miami a ranar Talatar ta makon gobe.

Ana dai tuhumar tsohon shugaban na Amurka da akalla laifuka bakwai, daga ciki har da kokarin yi wa shari'a katsalandan.

Babu dai wasu bayanan da suka fito kawo i zuwa yanzu daga ma'aikatar shari'a a Amurkar dangane da wannan tuhuma ta Donald Trump.

Sai dai da ma tana bincike kan sakacin da tsohon shugaban kasar ya yi da muhimman bayanan sirrin na gwamnati, bayan barin sa mulki a 2021.

Sama da takardu dubu 13 da aka kwaso daga gidansa da ke birnin Florida a bara, akwai guda 100 da suke dauke da muhimman bayanan gwamnatin.