1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump ya kada hantar kasashen Turai

February 13, 2024

Kalaman tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO ya tayar da kura a kasashen Turai. A yanzu kasashen Turan sun fara wani shirin ko-ta-kwana, ko da Trump zai dawo karagar mulki.

https://p.dw.com/p/4cMO4
Amurka | Donald Trump | NATO | Turai
Tsohon shugaban kasar Amurka Donald TrumpHoto: Nicholas Kamm/AFP

Tuni dai kalaman Donald Trump din, suka yi wa kungiyar Kwancen Tsaron ta NATO illa. Yayin gangamin yakin neman zabe a South Carolina ne Trump ya shaida wa mutanen da suka hallara cewa, a matsayin shugaban kasa ya gargadi kasashe kawayen NATO kan dukkan kasar da ba ta bayar da kason kudinta na tafiyar da harkar tsaro ba shi ma ba zai kasa a gwiwa ba wajen karfafa wa Rasha ta yi wa kasashen dukkan abin da ta ga dama.

Karin Bayani: Biden ya lashe zaben fidda gwani a Karolina ta Kudu

Wannan kalami ya tayar da kura a Turan, inda musamman ya kada hantar kasashe mambobin kungiyar ta NATO wadanda ba su biya nasu kason kudin ba. Kasashen dai na nuna damuwa kasancewar akwai yiwuwar Trump ya sake darewa kan karagar mulki. Sakataren kungiyar Kawancen Tsaron ta NATO Jens Stoltenberg ya ce duk wani tunani cewa kawancen kasashen ba za su bai wa junansu kariya ba, tamkar zagon kasa ne ga tsaronsu baki daya ciki har da ita kanta Amurkan. A cewasra, hakan zai jefa sojojin Amurka da na kungiyar Tarayyar Turai cikin hadari. A lokacin da yake shugaban kasa, Trump ya sha yin barazanar janyewa daga NATO.

Amurka | Donald Trump | Barazana | NATO | Jens Stoltenberg
Sakataren kungiyar Kwancen Tsaro ta NATO Jens StoltenbergHoto: picture alliance/Bill Clark/CQ Roll Call/Sipa USA

Ya ma yi kashedin cewa zai tilasta  kasashen Turan, su biya Amurka kariyar da ta ke basu. Wasu jakadu dai na ganin cewa, sake tayar da maganar da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi a wannan karon musamman a lokacin yakin neman zabe abin damuwa ne matuka. Wadanan kalamai na Trump sun zo a lokaci mawuyaci ga kungiyar Tarayyar Turai, inda karara wasu shugabannin ke gargadi na yiwuwar Rasha ta zafafa yakin da ta ke yi da Ukraine yayin da a waje guda majalisar dokokin Amurkan ta kawo tsaiko ga tallafin agajin Washington din zuwa Kyiv.

Karin Bayani: Trump ya daukaka kara zuwa kotun koli

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi kakkausar suka ga Trump ba tare da ya ambaci sunansa ba, dangane da kalaman da ya yi a kan NATO din. Sai dai kuma wasu shugabannin na Turai kamar firamnistar Eastonia Kaja Kalla na ganin cewa, idan an bugi jaki to sai abugi taiki suna masu cewa Trump fa yana da gaskiya idan ana magana ta gaggawa na bukatar kasashen Turai su kara zuba kudi wajen tsaro. Gwamnatoci a fadin nahiyar Turan dai ga alama sun fahimci cewa, akwai bukatar mambobin kasashen su kara azama wajen kare kansu ba tare da la'akari da ko wanene zai zama shugaban Amurka ba.