Nigeria ta dauki matakin tsaro a Niger Delta | Labarai | DW | 22.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nigeria ta dauki matakin tsaro a Niger Delta

Shugaba Olusegun Obasanjo na Nigeria ya umarci jamian tsaro a yankin Niger Delta mai arzikin mai dasu kwana cikin shiri don tunkarar duk wane kalubale na rashin tsaro daka iya tasowa.

A cewar mai magana da yawun fadar ta Nigeria, wato Remi Oyo cewa tayi shugaban ya bayar da wannan umarnin, bisa harin da aka kaiwa daya daga cikin manya manyan bututun mai na kamfanin shell a wani kauye dake jihar Fatakwal.

Wannan hari dai da aka kai a ranar litinin din data gabata, yayi asarar rayuka 11 a hannu daya kuma da kawo tsaiko game da yawan man da kamfanin ke samarwa a kullum ranar Allah ta´ala.

A waje daya kuma, rahotanni sun shaidar da cewa anyi musayar wuta a tsakanin jamian tsaro da wasu tsageru da ba a san suwa nene ba a kosa da ofishin majalisar dokokin jihar dake birnin Ibadan.

Rahotanni dai sun nunar da cewa musayar wutar ta biyo bayan, budewa wasu yan majalisar jihar ne wuta dake adawa da gwamnan jihar, wato Rashidi Ladoja a yayin da suke kokarin shiga zauren majalisar a yau alhamis.

Kafin dai shawo kann al´amarin , yan sandan sun dauki wasu yan awowi suna musayar alburusan a tsakanin su da mutanen.

A lokacin wannan dauki ba dadin, an kiyasta cewa mutane biyar ciki har da dan majalisa daya ne suka samu raunuka.