SiyasaJamus
Rasha za ta ladabtar da Jamus da Faransa
November 12, 2020Talla
Lavrov ya ce Jamus da Faransa sune suka yi uwa kuma suka yi makarbiya wurin takunkumin da kungiyar tarayyar Turai ta EU ta sanya wa manyan jami'an gwamnatin Rasha kan batun sanya wa jagoran adawar Rasha Alexei Navalny guba. Kazalika duk da zargin shugabannin Rasha da Jamus tayi kan shayar da Navalny guba, a wannan Alhamis ministan harkokin wajen Rashan ya yi ikirarin cewa su sun san cewa a cikin jirgin da Jamus ta dauko Navalny aka sanya wa jagoran adawar guba. To amma mai magana da yawun Navalny ta ce wannan wani nau'i ne na rainin hankali daga hukumomin Rasha.