1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

APC ko ADC- Wa zai yi zawarcin Kwankwaso?

Nasir Salisu Zango LMJ
October 22, 2025

Madugun Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya jadadda cewa, har yanzu yana kan bakansa na shimfida sharudda kafin shiga jam'iyyar APC ma mulki a Najeriya.

https://p.dw.com/p/52R6d
Najeriya | Kano | Siyasa | Kwankwasiyya | Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso
Jagoran Kwankwasiyya a Najeriya, Injiniya Dakta Rabiu Musa KwankwasoHoto: Nasiru Salisu Zango

Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, zai iya hadewa da Atiku Abubakar a ADC ko Tinubu a APC amma  dole akwai sharudda da ka'idoji. Kwankwaso wanda ake ci gaba da gabatar da bukukuwan murnar cikarsa shekaru 69 a duniya ya bayyana cewa, akwai alakar mutumtawa tsakaninsa da shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

Kwankwaso da ya kasance jagoran jam'iyyar adawa ta NNPP a Najeriyar, ya bayyana jin dadi bisa yadda Tinubun ya aiko masa da sakon taya murna har ma a cikin sakon ya jadadda tsohuwar alakarsu da kuma yadda suke da fahimtar juna.

Ko Kwankwaso zai shiga APC?

Amma fa wannan alaka ba tana nufin ya shiga jam'iyyarsa ba tare da sanin makomarsa da ta al'ummarsa ba, dan haka duk tafiyar da ta zo masa da tsari mai kyau na cikakkiyar makoma ga al'umma da magoya baya da shi kansa a shirye yake ya rungume ta a haye tudun mun tsira.

Ko waye zai lashe zaben Najeriya na 2023

Kwankwaso ya bayyana cewar babban abin da ke dagula masa zuciya a siyasar wannan lokaci shi ne cin amana, domin yaga darussa da dama na yadda mutane ke bijirewa gaskiya su rufe idanu wajen cin amanar wadanda suka cicciba su.

Alaka da gwamnatin Kano

Dangane da alakarsa da gwamnatin Kano wacce ya kafa kuma Kwankwasoya bayyana cewa, tafiyarsu tafiya ce ta yin biyayya ga tsarin Kwankwasiyyya da ke nufin inganta rayuwar alumma. A cewarsa dole ana tafiya ana bayar da shawarwari, domin tafiya ce ta amana.

Kwankwaso ya yi godiya, ga dubban mutanen da suka aiko masa da sakonnin taya murna a wannan lokaci. Wani abu da har yanzu ya shigewa mutane duhu dangane da matsayar madugun na Kwankwasiyya shi ne, rashin tabbas na ci gaba da zama a cikin jam'iyyar NNPP ko kuma ficewa da komawa jam'iyyar APC ko ADC ko kuma hadewa da Goodluck Jonathan su yi takara a jam'iyyar PDP.