1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ina jam'iyyar NNPP ta dosa?

Abdul-raheem Hassan Nasir Salisu Zango/LMJ
September 11, 2025

Rikicin siyasar cikin gida a jam'iyyar NNPP a jihar Kano, na iya sauya akalar zabe a 2027. NNPP wadda ta dauki Kano tamkar cibiyarta a Arewa, na fuskantar gagarumar barazana ta ficewar jiga-jiganta zuwa wasu jam'iyyu.

https://p.dw.com/p/50DjI
Najeriya | Kano | 2025 | Dakta Rabiu Musa Kwankwaso | Kwankwasiyya
Jagoran jam'iyyar NNPP a Kano, Dakta Rabiu Musa KwankwasoHoto: Nasiru Salisu Zango

A zaben 2023,jam'iyyar NNPP ta girgiza siyasar Najeriya da nasarar ba-zata da ta yi a Kano. Jam’iyyar ta lashe kujerar gwamna da mafi yawan kujerun majalisar dokoki, wanda ya tabbatar da tasirin Kwankwasiyya da karfin jagoranta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Jam'iyyar ta kuma lashe kujerara 'yan majalisa tsiraru a jihohin Bauchi, kana dan takararta ya zo na biyu a zaben gwana a jihar Taraba. Kwankwaso ya dauko jam’iyyar a matsayin mafita, ga miliyoyin matasa da ke neman canji daga tsofaffin jam’iyyu kamar APC da PDP. Amma bayan shekara biyu da cin zabe, abubuwa sun fara canzawa.

Yadda rikicin cikin gida ya raba jam'iyyar NNPP a Kano

Bayan gwamnatin NNPP ta tsaya da kafarta a Kano rikicin cikin gida ya soma ruruwa, inda har aka samu masu da'awar Abba tsaya da kafarka. Ma'ana, ya bar tafiyar uban gidansa Kwankwaso abin da ya haddasa korar sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Bappa Bichi.

Najeriya | Kano | 2025 | Dakta Rabiu Musa Kwankwaso | Abdullahi Umar Ganduje | Abdurrahaman Kawu Sumaila
Abdullahi Umar Ganduje da Abdulrahman Kawu SumailaHoto: Nasiru Salisu Zango

Bappa Bichi ya koma APC, jam’iyyar NNPP ta rasa wasu 'yan majalisu da suka ci zabe da farin jininta. Wasu sun koma APC wasu PDP, yayin da wasu kuma ke jiran zaman yadda za ta kaya a jam'iyyar PDP.

Wannan matsala dai, ana danganta ta da rashin jituwa tsakanin bangaren Kwankwasiyya da sauran shugabannin jam’iyyar a matakin kasa da kuma jiha.

'Yan majalisun da suka fice daga NNPP

Kabiru Alhassan Rurum daga matsabar Rano da Kibiya da Bunkure da AbdullahI Sani Rogo wanda ke wakiltar Karaye da Rogo sai kuma Ali Sani Madakin Gini daga mazabar Dala, baya ga Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila na Kano ta Kudu da ma dan majalisar jiha na Sumaila wato Zubairu Hamza Massu sun fice daga NNPP.

Wannan na nuna cewa jam’iyyar na rasa turbar da ta ginu a kai a 2023, wanda ka iya zama babban kalubale ga Kwankwaso da burinsa da kuma tasirinsa a zaben 2027.

Kwankwaso da Ganduje: Siyasar Kano ta yi zafi

Tasirin rikicin NNPP ga makomar Kwankwaso a 2027

Sanata Rabi'a Musa Kwankwaso fitaccen dan siyasa ne da ya saba fuskantar kalubale a fagen siyasa, amma wannan rikici na cikin gida da ficewar jiga-jigan jam'iyyar na iya kawo cikas ga burinsa na takara ko zawarci da babban dan takarar da zai nemi kuri'un jihar Kano da nufin cin zabe a 2027. Ko da yake wasu na ganin yunkurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa, tamkar ba ta ruwa ne ba don a sha ba.

Wanne kalubale Kwankwaso zai iya fuskanta?

Rasa kwamandojin 'yan siyasa daga tushe: Raba gari da kusoshin jam'iyyar NNPP suka yi, kamar su Suleiman Abdurrahaman Kawu Sumaila da Abdulmumin Jibrin Kofa na nuna alamun karya agon tasirin siyasar Kwankwaso ne a 2027.

Najeriya | Kano 2025 | Kawu Sumaila | Abdulmumin Jibril Kofa | Kabir Alhassan Rurum
Sanata Kawu Sumaila da Abdulmumin Jibril Kofa da Kabir Alhassan RurumHoto: Nasiru Salisu Zango

Raguwar kwarin guiwar masu zabe: Wadanda suka zabi NNPP a 2023 suna iya sauya ra’ayi, muddin suka ga jam’iyyar na cikin rikici da baraka. Da dama na iya hasashen cewa, sarkin yawa zai iya fin sarkin karfi. 

Matsalar hadin kai: Idan Kwankwaso bai iya daidaita jam’iyyarsa a Kano kafin babban zaben shekarar 2027 ba, zai yi wahala ya samu hadin kai a matakin kasa. Yana bukatar dunkule manyan 'yan siyasa masu tasiri a jihar, abin da zai ba shi damar murza kambunsa tsakanin 'yan takarar shugaban kasa.

Kalubalen shari'a da abokan hamayya: Yadda jam'iyyar APC ta kalubalanci Abba Kabir Yusuf a kotu, zai sake bai wa abokan hamayya karfin gwiwar kalubalantar NNPP a Kano da Arewa baki daya.

Shin har yanzu Kwnkwaso na da sauran dama?

Duk da kalubalen da tsohon gwamnan Kanon ke fuskanta, ya yi wuri a iya yi masa yankan kauna kasancewar siyasa tamkar wasan kwallon ne. A dangane da haka, ba za a iya cewa burin Kwankwaso ya disashe ba. Gagarumin goyon bayan da ya ke da shi daga matasa da iya takunsa a fagen siyasa da kuma tarihi mai tsawo na nasarorin da ya cimma, tubali ne ga makomarsa a siyasance.

Ko waye zai lashe zaben Najeriya na 2023

Zargin Kwankwaso da nuna fifiko musamman a tsayawa 'yan Arewa: 'Yan Arewa na shafar tasirin siyasarsa a kudancin Najeriya, musamman yadda ake ganin kowane dan takarar shugaban kasa yana bukatar goyon baya daga duka bangarorin kasar.

Don haka Kwankwaso na bukatar kawar da wadannan kalubale da ke tare masa hanyar cimma burinsa a zaben 2027, kadan daga ciki shi ne sake dinke barakar jam'iyyar NNPP da karfafa tsarin jam’iyyar daga kasa zuwa sama. Sanna akwai bukatar inganta alakarsa da sauran ‘yan siyasar Arewa da Najeriya baki daya, uwa uba bullo da sababbin manufofin sake jawo hankalin jama'a kamar yadda ya yi a 2023.

Najeriya | Kano | 2025 | Dakta Rabiu Musa Kwankwaso | Kwankwasiyya
Jagoran Kwankwasiyya da jam'iyyar NNPP a Kano, Dakta Rabiu Musa KwankwasoHoto: Nasiru Salisu Zango

Wanne tasiri Kano ke da shi a zaben 2027?

Kamar yadda ake cewa: "Duk wanda ya samu kuri'un Kano, ya samu Arewa", haka nan siyasar Najeriya ke tafiya tun bayan dawowar mulkin dimukuradiyya a 1990. Jihar Kano, na da yawan kuri’u da tasiri sosai a zaben Najeriya. Idan NNPP ta rushe a Kano, to Kwankwaso zai fuskanci babban kalubale a 2027.

Amma idan aka yi saurin dinke barakar, har yanzu akwai fata cewa Kwankwaso zai iya mayar da karfinsa da tasirinsa a matakin kasa.

Shin Kwankwaso zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, ko zai bi guguwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko kuwa zai jera ne a sabuwar tafiyar ta ADC?

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani