Zargin Kwankwaso da neman yin katsalandan a shugabancin Kano | Siyasa | DW | 29.03.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zargin Kwankwaso da neman yin katsalandan a shugabancin Kano

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi watsi da zargin cewa, zai nemi yin katsalandan a harkokin shugabancin jihar Kano.

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso

A Najeriya, jagoran jam'iyyar NNPP wacce ta lashe zaben gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da zargin da ake masa na shirya yi wa zababben gwamnan jihar katsalandan a harkokin shugabanci.

A cikin wata kebabbiyar hirarsa da Sashen Hausa na DW, Kwankwaso ya ce, wannan zargin ba zai hana shi ya bai wa gwamnan Kano mai jiran gado Abba Kabir Yusuf, shawarar da ta dace domin ciyar da jihar gaba ba. 

Wannan na zuwa ne bayan da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Najeriyar wato INEC, ta tabbatar tare da mika wa Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar ta NNPP shedar lashe zaben gwamnan jihar Kano; na zaben gwamnonin da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na wannan shekarar ta 2023.

Sauti da bidiyo akan labarin