1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwankwaso ya bar PDP zuwa Jam'iyyar NNPP

Uwais Abubakar Idris
March 30, 2022

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da ficewa daga jam'iyyar PDP a hukumance tare da baiyana komawa sabuwar jam'iyyar NNPP

https://p.dw.com/p/49FX4
DW l Kwankwaso Interview, Nigeria
Hoto: Kwankwasiyya official Foto, Kano Nigeria

A Najeriya tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da ficewa daga jamiyyar adawa ta PDP tare da shiga sabuwar jamiyyar New Nigeria Peoples Party watau NNPP.

Kwankwaso ya dauki wannan mataki ne 'yan sa'oi sabuwar jamiyyar ta gudanar da babban taronta a Abuja domin zaben shugabani da za su ja ragamarta da ma fafafatwa a babban zaben da za’a yi a badi a Najeriya.

Tsohon gwamnan na Kano da ke jagorantar tafiyar Kwankwasiyya ya nemi takarar shugaban kasa a 2015 a zaben fidda gwamani karkashin inuwar jamiyyar adawa ta PDP.

Ana iya sauraron hirarsa da wakilin mu Uwais Abubakar Idris