Kwankwaso dan siyasa ne da ya fito daga jihar Kano a Tarayyar Najeriya wanda aka haifa a shekaar 1956. Ya yi gwamna a jihar tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003.
Baya ga gwamna ya kuma rike mukami na minsitan tsaro a wa'adi na biyu na gwamnatin Obasanjo sannan ya sake mulkar Kano a matsayin gwamna tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015 kafin daga bisani a zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya.