Gwamnati ta yi biris da kisan masu zanga-zanga
October 21, 2020Kama daga tsohon shugaban Najeriyar Olusegun Obasanjo da ke rubuta wasika ya zuwa ragowar dattawa da ma masu tunani game makomar Tarayya Najeriyar dai, kone-konen na birnin legas sun tayar da hankalin al'umma ta kasar. To sai dai kuma majalisar zartarwar Tarayyar Najeriyar ta zabi karatun kurma game da sabon yanayin da ya kalli kone kadarori na hukumomin Najeriya da na birnin Legas din ko bayan jiga-jigai na birnin da ke ji a jiki.
Karin Bayani: Gwamnati za ta kula da 'yan sanda a Najeriya
Maimakon mai da hankali ga zanga-zangar ta Ikko dai, ministocin sun dauki lokaci suna batun inganta maganin gargajiya tsakanin al'umma ta kasar a fadar Osagie Ehinare da ke zaman minista na lafiyar kasar: "Ma'aikatar lafiya ta gabatar da bukatar kafa majalisar inganta maganin gargajiya a Najeriya."
Shirun ministocin dai a fadar majiyoyin zauren taron na da ruwa da tsaki da kokarin kaucewa tayar da hankalin al'ummar kasar da wasunsu ke da zuciyar mai tsumma. To sai dai kuma majiyoyin sun ce an umarci ministocin da su tattauna da masu ruwa da tsaki a harkokin matasa a jihohinsu, domin tabbatar da kwantar d hankulan al'umma da kaucewa sake maimaita ta'asar kisan 'yan #EndSARS
a birnin Legas. Ya zuwa yanzu dai kungiyoyi na ciki da ma wajen Najeriyar da kuma kasashe, na mai da martani ga tashe-tashen hankalin na birnin Legas da suka hada da zargi na kisa na masu zanga zangar kare SARS.
Karin Bayani: Gwamantin Najeriya ta baza sojoji
Ita kanta jam'iyyar PDP ta adawa dai, ta ce kau da ido na hukumomin na kama da kokari na lullube kura a cikin fatar rago. Kura a cikin fatar rago ko kuma kokari na tayar da hankalin al'umma, in har tashin hankalin birnin Legas din ya tayar da hankali ga masu adawa dai, ita ma APC na kallon neman korar SARS din bai wuce kokarin ta'annati cikin kasar ba, a fadar Ibrahim Masari da ke zaman jigo a jam'iyyar ta APC da ke mulki, da kuma ya ce an kai bango kuma hakuri na 'yan kasar na shirin da ya kare.
Karin Bayani: Fargaba kan zanga-zangar da ke wakana a Najeriya
Ko ya zuwa yaushe take shirin kai wa tik din dai, a wannan Alhamis din ne aka tsara taron majalisar tsaron kasar da nufin sanin mataki na gaba ga Tarayyar Najeriyar da 'ya'yanta ke kirga asara a matakai dabam-dabam cikin kasar, sakamakon tawayen na matasa.