Najeriya: An soma bincike kan kisan 'yan #EndSARS | Labarai | DW | 21.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An soma bincike kan kisan 'yan #EndSARS

Gwamnatin jihar Legas ta kaddamar da bincike kan kisan masu zanga-zanga a yankin Lekki a daren ranar Talata. Rahotanni na cewa mutum kusan ashirin ne suka mutu bayan da jami'an soja suka bude musu wuta.

Gwamnatin jihar Legas a Najeriya ta ce za ta kaddamar da bincike a game da kisan masu zanga- zanga a sakamakon bude musu wuta da aka ce sojoji sun yi a jiya Talata. Al'ummar Najeriya sun kwana da jimami a sakamakon hargitsin da ya biyo bayan zuwan sojojin a dandalin da ke Lekki. Batun da ya janyo suka da kuma alhini a ciki da ma wajen kasar. 

Kungiyar Amnesty International ta ce akwai rahotanni da ke tabbatar da kisan masu zanga-zangar a sanadiyar harbe-harben sojoji sai dai kawo yanzu rundunar sojin kasar ba ta ce komai ba. Hargitsin dai ya biyo bayan bijirewa dokar gwamnatin jihar da masu zanga-zangar suka yi na hana fita bayan da aka kona wani ofishin yan sanda.