1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magungunan gargajiya na illa a Najeriya

June 4, 2014

Likitoci da kwararru a bangaren kiwon lafiya a Najeriya sun gargadi al'umma game da hatsarin da ke tattare da shaye-shayen magungunan gargajiya ba bisa ka'i'da ba.

https://p.dw.com/p/1CCHd
Hoto: DW/S. Boukari

Likitoci sun fara fitowa ta kafafen watsa labarai wajen janyo hankali al'umma game da matsalolin shan magungunan gargajiya ba bisa kima ba. Doctor Prince Audu daga asibitin Lasa a Nigeria ya ce " hanyoyin da suke bi wajen sarrafa wadannan magunguna ya kamata a canjata, ta hanyar tsaftace itacen da suke hakowa da kuma ganyen da suke amfani da shi"

Jami'an kiwon lafiya sun bayar da tabbacin cewa shan magunguna ba bisa tsari ba na janyo mutuwar zuciya, da lalacewar koda da hanta. Hatta ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya fitowa fili ta yi ta nuna rashin gamsuwarta game da irin ayyukan da masu magungunan gargajiya ke aikatawa a cikin kasar. Ta ce sun kasa yin amfani da hanyoyin kimiyyar zamani wajen tantance cutar da ke damun marasa lafiya.

Malam Danladi Musa wani mai maganin gargajiya ne a Nijeriya. ya yi kira ga "hukumomi su taimaka mana maimakon kushe aikinmu da suke yi akai-akai kan batun magungunan da muke bai wa al'umma da suke samun sauki." Su ma dai 'yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu inda wasu ke nuna jin dadinsu game da magungunan gargajiya da suke sha. Amma wasu kuwa kushe magungunan suke yi a ko da yaushe.

Nigeria Impfung Kinder Kind
Hukumomin Nijeriya suka ce a fifita yin rigafiHoto: AFP/Getty Images

Kungiyoyin sun bukaci ganin gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kara rubanya kokarin da take yi wajen inganta asibitocin kananan hukumomi da kuma bullo da hanyoyin taimaka wa masu magungunan gargajiya da kayayyakin inganta sana'ar bayar da magunguna da suka yi gado daga iyayensu.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe