1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasa ta kankama a Najeriya

Mouhamadou Awal Balarabe
February 7, 2019

A lokacin da aski ya fara isowa gaban goshi dangane da zaben shugaban kasa a Najeriya, 'yan takara ciki har da Buhari na APC da Atiku na PDP na jan hankalin jama'a kan ayyukan da za su gudanar idan suka samu nasara.

https://p.dw.com/p/3CuPZ
Vor Wahlen in Nigeria  Muhamadu Buhari (M), Präsident von Nigeria, und Atiku Abubakar (r)
Hoto: picture-alliance/AP/B. Curtis

Fannoni na tattalin arziki da tsaro da yaki da cin hanci na taka muhimmiyar rawa a yakin neman zaben shugaban kasa da zai gudana ranar 16 ga wannan wata. saboda haka ne 'yan takara dabam-daban ke kewayawa sako da lungu na kasar don tallata manufofinsu ga 'yan Najeriya da nufin samun kuri'unsu. DW ta shirya jerin rahotanni kan fannoni da dama kuma daga jihohi dabam-daban a kan wannan zabe .