Najeriya: Farfagandar yaki da cin hanci gabannin zabe | Siyasa | DW | 31.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Farfagandar yaki da cin hanci gabannin zabe

Jama'a sun fara mayar da martani ga dabarun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar wanda ya ce zai yi yafiya ga barayin biron da suka sace kudade amma kuma suka dawo da su.

Atiku Abubakar din dai ya ce yana da niyyar sauyin tsarin yaki da cin hancin Najeriya tare da yin afuwa ga barayin biron da suka amince domin dawo da kudaden. A fada ta madugu na adawar dai wannan tsari ya yi aiki a tsohuwar gwamnatin kasar inda suka dawo da sama da Dalar Amirka miliyan dubu hudu, sannan kuma yana zaman kashin bayan sake ginia Turkiya. Duk da cewar dai tsarin ya yi aiki a tsohuwar gwamnatin Olusegun Obasanjo, daga dukkan alamu kuma ya gaza ga gwamnatin Yar ‘Aduwa da ma 'yar uwarta ta Jonathan da ta shude a fadar Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman shugaban kungiyar Transparency reshen Nigeria mai yakar cin hanci a kasar.

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin