Najeriya: Atiku zai yi afuwa ga barayin kasa | Labarai | DW | 31.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Atiku zai yi afuwa ga barayin kasa

A Najeriya dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP a zabe mai zuwa Atiku Abubakar, ya sha alwashin idan ya ci zabe yin afuwa ga duk barayin kasa da suka amince su maido da kudin da suka sata. 

Vize Präsident Atiku Abubakar, Nigeria (AP Photo)

Atiku Abubakar ya bayyana wannan aniya tasa ce a wata fira da wata tashar talabijin a yammacin jiya laraba inda ya ce irin wannan mataki na afuwa ya yi tasiri a kasar Turkiyya wace ta yi nasarar karbo illahirin kudadenta da aka sata aka kai kasahen ketare. 

Kazalika dan takarar jam'iyyar adawar a zaben shugaban kasa na 16 ga watan Febuari ya zargi tsarin shari'ar Najeriya da kasancewa dalilin jan kafar da ake fuskanta a fagen yaki da cin hanci. 

Sai dai shi kansa Alhaji Atiku Abubakar mai shekaru 72 hamshakin dan kasuwa wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa, mutun ne da ya yi kaurin suna a Najeriya inda jama'a da dama ke kallonsa a matsayin dan siyasar da ya fi kowa cin hanci da kuma ya yi amfani da matsayinsa na siyasa wajen wawure dukiyar Najeriyar tsakanin shekara ta 1999 zuwa 2007, zargin da ya sha musantawa.