1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajen Jamus ya isa a birnin al-Ƙahira.

July 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bupe

Ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier, ya fara wata ziyara a Gabas Ta Tsakiya, da burin ƙiƙiro wani yunƙuri na diplomasiyya don kwantad da ƙurar rikici a yankin. Ministan ya fara ya da zango ne a birnin al-Ƙahira, inda ya gana da takwaran aikinsa na ƙasar Masar Ahmed Abul Gheit. A gun taron maneman labaran da suka kira bayan ganawar tasu, Steinmeier ya ce bai kamata a bai wa ’yan tsageru damar jan akalar ababan da ke wakana a Gabas Ta Tsakiyan ba. Amma ya kuma nanata cewa, ba ƙoƙari Jamus ke yi ta zamo mai shiga tsakani a lamarin yankin ba. Daga Masar ɗin dai, ministan harkokin wajen na Jamus, zai tashi ne zuwa Isra’ila, inda zai gana da Firamiya Ehud Olemrt, sa’annan daga bisani kuma, da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, kafin ya dawo gida.