Merkel na tattauna batun Ukraine a Washington | Labarai | DW | 09.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel na tattauna batun Ukraine a Washington

Shugabar gwamnatin ta Jamus tana tattuana batun rikicin gabashin Ukraine da Shugaba Barack Obama na Amirka.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da yanzu haka take birnin birnin Washington ta fara tattaunawa da shugaban Amirka Barack Obama a fadar White House. Tattaunawar tana mayar da hankali a kan sabon yunkurin da Jamus da Faransa ke yi na warware rikicin Ukraine cikin lumana. Wani abin da taron na wannan Litinin yake kuma dubawa shi ne makaman yaki da Amirka za ta tura wa sojojin Ukraine. Merkel dai na adawa da wannan mataki. A kwanakin bayan nan dai 'yan jam'iyyar Republicans sun yi kira da a tura wa Ukraine makamai a yakin da take yi da 'yan awaren gabashin kasar masu goyon bayan Rasha.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo