Merkel na ganawa da SPD kan kafa gwamnati | Siyasa | DW | 08.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Merkel na ganawa da SPD kan kafa gwamnati

Kawancen jam'iyyar Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta CDU/CSU da tsohuwar abokiyar kawancen gwamnatinsu SPD na tattauna batun kafa sabuwar gwamnati tare da makomar Kungiyar Tarayyar Turai.

Shugabannin jam'iyyun Merkel daga jam'iyyar CDU da kawarta ta jihar Bavaria CSU da jam'iyyar ta SPD sun yi zama na biyu don tattauna batun kafa gwamnati, inda manyan batutuwa da suka hada da gamayyar kasashen Turai za su mamaye ganawar, kamar yadda Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana.

"Kawancen CDU/CSU ya mayar da hankali ne wajen ganin an samu gwamnati da ta tsaya da kafarta, mun amince muna da kalubale a gabanmu kuma wannan alhaki ne ya rataya a wuyanmu. Haka batu na tsare-tsare tsakanin kasashen Turai da siyasar kasashen, muna so mu kafa ginshiki na tafiyar da harkokin gwamnati shekaru biyar ko ma zuwa goma a zauna lafiya demokradiya ta daidaita."

A cewar Merkel dai babban abin da ke gabansu na zama samun fahimta da al'umma musamman a wannan lokaci da ake samun ci gaba na fasaha, ga kalubale na tsaro na cikin gida da waje, ta ce ba za su kai ga cimma burin da suke so ba a duniya idan babu hadin kai tsakanin kasashen Turai musamman kan batutuwa da tsare-tsarensu da suka shafi 'yan gudun hijira abin da take da fata na samun nasara bisa aiki tukuru.

"Ina ganin zamu yi nasara idan muka shiga aiki ba kakkautawa tare da sanya al'ummar Jamus a zuciyarmu, mu ga mun biya masu bukatunsu a matsayinmu na 'yan siyasa da suke da fata a kanmu, na shiga wannan tattaunawa ne don samun mafita kan matsalolin al'umma kuma ina sa rai zamu yi aiki tukuru fatanmu dai shi ne a samu sakamako mai kyau."

'Yan siyasar Jamus na ganin akwai bukatar aiki cikin gaggawa wajen ganin kafuwar gwamnatin hadakar da a baya jam'iyyar Social Democrats ko SPD ta ce a je ayi ba da ita ba, sakamakon munin kayin da ta sha a zaben da aka yi ranar 24 ga watan Satumbar bara, inda ta koma gefe tana kallon jam'iyar ta Merkel CDU na kokarin kafa gwamnati da wasu kananan jam'iyyun adawa, don haka matakin da aka kawo yanzu ya sa dole a yi azama a cewar Martin Schulz, shugaban jam'iyyar SPD.

Berlin Bundesparteitag SPD Martin Schulz (picture-alliance/AP Photo/M. Schreiber)

Dan takarar jam'iyar SPD, Martin Schulz

"Mun lura cewa bayan zaben da aka yi a Jamus, yunkurin hadakar jam'iyyun JAMAICA sun dauki makonni Takwas, bai kamata mu dauki lokaci mai tsawo ba yanzu, zamu kai ga karshe cikin kwanaki biyar da ke tafe muna da abubuwa da dama da ra'ayinmu yazo daya hakan zai taimaka wajen shiga gwamnatin hadaka. Kamar yadda aka sani ne wannan abu ne da za a cimma a babban taron jam'iyyarmu. Ina da yakini cewa kowa a shirye yake ga shirin shiga tattaunawar don haka ne na yiwa bakinmu maraba."

Ana ganin tsawon lokacin da jam'iyyun kasar Jamus suka dauka kafin kafa gwamnati bayan zabe da ya zama mafi tsayi a kasar tun bayan yakin duniya na biyu na iya zuwa karshe a wannan karo, saboda bukatar gwamnatin Jamus ko dan motsawar lamura a tsakanin kasashren Turai ganin ko bayan zaben da aka yi a watan Satumbar a nan Jamus Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya gabatar da tsare-tsare kan makomar Kungiyar Tarayyar Turai. Sai dai yana dakon ji daga bangaren Jamus wacce ke taka muhimmiyar rawa a harkokin kungiyar ta EU.