Merkel: ″Kada a bada muhimmanci ga sabani da Amirka kan sauyin yanayi″ | Labarai | DW | 29.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel: "Kada a bada muhimmanci ga sabani da Amirka kan sauyin yanayi"

Amirka dai ta nemi a bata karin lokaci domin ta yi nazari kan manufofinta na sauyin yanayi kafin ta yanke shawara kan yarjejeniyar Paris.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ba daidai ba ne a mayar da hankali kan sabanin da aka samu da Amirka kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, tana mai cewa taron kolin kungiyar G7 da ya gudana a karshen mako ya nuna karara zai yi wahala a samu nasara kan yarjejeniyar birnin Paris da ta shafi sauyin yanayi.

Shugaban Amirka Donald Trump ya ki amincewa da ka'aidojin yarjejeniyar muhallin a taron na kasashe mafi karfin tattalin arziki a duniya da ya gudana karshen mako a kasar Italiya, inda ya nemi karin lokaci kafin ya yanke shawara.

A lokacin da take magana a gun wani babban taro kan ci-gaba mai dorewa a birnin Berlin, Merkel ta jaddada matsayinta cewa ba za a iya dogaro kan abokan kawance a kowane lokaci ba, dole kasashen Turai su dauki makomarsu a hannunsu. Wannan furucin dai ya zo wa gwamnatocin biranen Washington da London da mamaki.