Martanin duniya kan harin Tunisiya | Siyasa | DW | 19.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin duniya kan harin Tunisiya

Ƙasahen duniya na ci gaba da yi Allah wadai da harin ta'addanci da a kai a wani gidan addana kayan tarihi dake a kasar Tunis inda mutane 19 suka mutu wasu 44 suka jikkata

Ciki mutane 19 da suka mutu 17 baki masu yawon bude ido ne, yayinda biyu kuwa yan kasar ta Tunisiya ne. Suma dai shaidu wadanda suka tsira daga farmakin sun bayyana halin da suka tsintsi kansu a ciki.

An kwashe kusan sa'o'i hudu 'yan bindigan na bude wuta a kan gine ginen gidan tarihin, inda suka rutsa da wasu mutane sama da 100, wadanda suka yi garkuwa da su.

Wannan matar mai suna Carrole 'yar kimani shekaru 40, wacce ta zo daga kasar Faransa tana daga cikin wadanda hare-haren suka afku a kan idanunta, a sailin da take ziyarar gidan addana kayan tarihin ga kuma abinda ta ke cewa.

"Mun kwashe kusan sa'a daya muna kwance a kas ba mai yin motsi, har sai lokacin da jami'an tsaro suka zo. A lokacin ne aka ce mana, ku fita-ku-fita da gudu ku bar nan".Mutane dai 19 suka mutu yayin da jami'an kwana-kwana suka yi ta kwashe wadanda suka jikkata daga gidan tarihin dake kusa da majalisar dokoki zuwa asibiti, domin samun kulawa. Take-yanke dai a lokacin harin jami'an tsaro suka bindige wasu daga cikin maharan har lahira. Daga cikin wadanda suka mutu har da 'yan kasashen Japan guda uku da Italiyawa suma mutane uku da Sipaniyawa guda biyu da Kwalambiya da Faransawa guda biyu.

A cikin wata sanarwa da ya bayyana ta gidan talabijin na kasar, shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi, ya ce ba za su yi da wasa ba ga 'yan ta'addan.

"Ya ce zamu kara karfafa gwiwar jami'an tsaronmu da kuma abin da ya shafi harkokin tsaro, domin takawa 'yan ta'addan birki. Sannan muna kira ga 'yan Tunisiya, da su bada gudumowarsu wajen tantance miyagun mutane"

A halin da ake cikin kasahen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da hare-haren. A sanarwa da ya bayyana sakataran harkokin wajen Amirka John Kerry, ya bayyana takaicinsa tare da jinjinawa hukumomin Tunisiyasa, dangane da yadda suka mayar da martani da gaggawa a kan hare-haren.Haka shi ma babban sakataran kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, da babban sakataran Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon duk sun yi tsokaci a ka lamari, inda Ban Ki-moon, ya bukaci da a gurfanar da wadanda suka aikata ta'asar a gaban kuliya. Yayin da ita ma kungiyar Tarayyar Turai, ta ce babu gudu-babu ja da baya wajen yaki da ta'addanci, da kuma dauki da take kokarin baiwa kasar Tunisiya na samar da cikakkakiyar demokradiyya.

Shi kuwa shugaban kasar Faransa Francois Hollande, cewa ya yi "Duk lokacin da aka kai harin ta'addanci, to mu dukka wannan abu yakan shafemu"

A kasar ta Tunisiya dai safiyar yau Alhamis, ofishin ministan cikin gida, ya ce an gano wasu mutane guda biyu wadanda aka kai harin tare da su. Inda bada sunayensu kamar haka, Yassine Abidi da Hatem Khachnaoui. Sai dai babu wani karin bayyani da ofishin ya bayar a kansu. Amma a wata sanarwa da kungiya 'yan ta'adda wanda aka sani IS ta fitar, ta dauki alhakin kai harin na kasar Tunisiya da aka kai ranar Laraba.