Frank-Walter Steinmeier dai shi ne ministan harkokin wajen Jamus. Sau biyu ya taba rike wannan mukami a rayuwarsa.
An haifeshi a ranar 5 ga watan Janairun 1956. Shi ma jigo ne a jam'iyyar SPD da ke da matsakaicin ra'ayin gurguzu. Ya fara ministan harkokin wajen Jamus karkashin gwamntin Gerhard Schröder.