Manufofin cikin gida na Jamus a 2003 | Siyasa | DW | 24.12.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin cikin gida na Jamus a 2003

Bayan kamawar shekarar ta 2003 hankali ya koma ne kacokam akan barazanar da Amurka take yi na katsalandan soja a Iraki. Shi kuma shugaban gwamnatin Jamus tun da farkon fari ya fito fili ya bayyana cewar kasar ba zata shigar da sojojinta a wannan mataki ba. Kuma ko da shi ke kasashe kamar Faransa da Rasha na dauke da irin wannan ra'ayi, amma Amurka ta kalubalanci Jamus da kakkausan harshe akan wannan matsayi da ta dauka. An fuskanci gurbacewar yanayin dangantaku tsakanin kasashen biyu, amma gwamnatin hadin guiwa ta SPD da the Greens ta samu cikakken goyan baya daga sauran al'umar kasa a game da wannan matsayi da ta dage akansa. To sai dai kuma duk da wannan goyan baya jam'iyyar SPD ta kwashi kashinta a hannu a zabubbukan da aka gudanar a jihohin Hesse da Lower Saxony a cikin watan fabarairun da ya gabata. A can Hesse jam'iyyar tayi asarar kashi 10% na kuri'unta a yayinda CDU ta samu karin kashi 5% ta kuma tashi da gagarumin rinjaye na kashi 49% na jumullar kuri'un da aka kada. A can jihar Lower Saxony kuwa jam'iyyar ta SPD tayi asarar abin da ya kai kashi 15% a yayinda CDU ta samu karin kashi 12% domin kafa gwamnatin hadin guiwa tsakaninta da FDP bayan shekaru 13 a matsayin 'yan hamayya a wannan jiha. Jam'iyyar ta CDU ta ci gaba da samun nasarori a zabubbukan jiha da na kananan hukumomi a wannan shekarar mai karewa. Daya abin da ya dauki hankalin jama'a a game da manufofin cikin gida na Jamus kuma shi ne matsalar jami'in siyasar nan na FDP Jürgen Möllemann, wanda ya fara karkata zuwa ga kyamar Yahudawa. Jim kadan kafin zaben majalisar dokoki ta Bundestag jami'in siyasar ya gabatar da wasu kasidu dake kunshe da batutuwa na cin zarafin yahudawa. Bayan kai ruwa rana da aka sha famar yi tsakaninsa da sauran 'ya'yan jam'iyyar ta FDP, jami'in siyasar ya tsayar da shawarar ficewa daga tutar jam'iyyar kuma ya bakunci lahira sakamakon hatsarin laimar sauka daga jirgin sama, wanda ake ikirarin cewar shi ne ya kashe kansa da kansa. Dangane da batutuwan siyasa kuwa hankali ya fi karkata ne zuwa ga shirin garambawul ga tsarin kyautata jin dadin rayuwar jama'a da gwamnati ta tanadar. A daidai ranar 14 ga watan maris shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya gabatar da sanarwar manufofin gwamnatinsa ga majalisar dokoki ta Bundestag inda yake kiran nuna karfin halin tinkarar canje-canje, domin ta haka ne kawai tattalin arzikin kasar ta Jamus zai sarara daga koma bayan da ya dade yana fuskanta. Matakin nasa sun hada da rage yawan abin da kamfanoni ke kashewa akan ma'aikata saboda a samu kafar shawo kan matsalar nan ta rashin aikin yi da ta ki ci ta ki cinyewa. Da wannan bayanin Schröder ya gabatar da matakinsa na garambawul mai taken ajenda 2010. To sai dai kuma a yayinda 'yan kasuwa da 'yan hamayya ke korafin cewar wannan shirin bai taka kara ya karya ba, su kuma masu ra'ayin gurguzu na jam'iyyar SPD da kungiyoyin kodago sun yi zargi ne cewar shugaban gwamnatin ya nemi wuce gona da iri a game da tsauraran manufofin da shirin nasa ya tanada. Shugaban uwar kungiyoyin kodagon Jamus ta DGB Michael Sommer yayi nuni da cewar wannan shawara tana bukatar gyara. Wannan lafazi nasa ya sosa wa 'ya'yan SPD dake adawa da shawarar daidai inda ke musu kaikai, inda suka rika fafutukar fatali da kundin, wanda aka samu daidaituwar baki kansa tare da 'yan hamayya na Christian Union. Ala-tilas aka kira babban taron jam'iyyar ta SPD na musamman, wanda a ranar daya ga watan yuni ya amince da shawarar ta gwamnati. Su ma 'ya'yan jam'iyyar hadin guiwa ta the Greens sun ba wa shirin goyan baya a taro na musamman da suka gudanar domin shawartawa kansa. To sai dai kuma gwamnati ba ta samu cikakken goyan baya da take bukata daga majalisar gwamnonin jiha ta Bundesrat domin wanzar da dokokin garambawul din ba, sai bayan da kwamitin shiga tsakani da aka nada ya sa baki tukuna. Amma a daya bangaren an cimma daidaituwa tsakanin illahirin jam'iyyun siyasar Jamus akan maganar haramta jam'iyyar nan mai zazzafan ra'ayin kyamar baki ta NPD, wacce ke goyan bayan akidar wariya ta Hitler. Dukkan majalisun gwamnoni ta Bundesrat da ta dokoki Bundestag da kuma gwamnati sun yi hadin guiwa domin gabatar da kararsu gaban kotun koli dake Karlsruhe. To sai dai kuma an dakatar da shari'ar bisa zargin mahukunta da laifin shigar da jami'an leken asirinsu tsakanin 'ya'yan jam'iyyar a daidai lokacin da ake kan hanyar cin shari'ar, wanda lamarin ne da ya saba da dokokin tsarin mulkin kasa. Wannan maganar ta ta da hankalin jama'a matuka ainun ko da shi ke kwanaki biyu kacal bayan haka hankali ya sake karkata zuwa ga kasar Iraki, wadda sojojin Amurka da na Birtaniya suka fara kai mata hare-hare. A cikin wani jawabin da ya gabatar ta telebijin shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya bayyana takaicinsa a game da wannan mataki da kasashen biyu suka dauka a maimakon neman shawo kan rikicin da ake ciki a cikin ruwan sanyi. Kwanaki kadan bayan haka ne kuma manazarta suka sake maido da hankalinsu zuwa jihar Bremen, wacce ke shirye-shiryen zabe. Godiya ta tabbata ga farin jinin da dan takarar SPD Henning Scherf ke da shi tsakanin al'umar wannan jiha, jam'iyyar ta samu gagarumar nasara. Amma kuma ko da shi ke jam'iyyar CDU ta fuskanci mummunan koma baya, amma Henning Scherf bai dadara ba yana mai ci gaba da mulkin hadin guiwa da jam'iyyar a wannan jiha. To sai dai kuma duk da wannan nasara jam'iyyar SPD ta ci gaba da fuskantar koma baya, inda binciken ra'ayin jama'a ya ba ta goyan baya na kashi 30% kacal da za a gudanar da wani sabon zabe a nan kasar. A yanzun ba abin da yayi shaura illa a sa ido a ga yadda al'amura zasu kaya a sabuwar shekara mai kamawa ta 2004, wadda ita ma din take kunshe da zabubbuka na jihohi da kananan hukumomi, wadanda kuma ba shakka maganar garambawul ga tsarin jin dadin rayuwar jama'a zata taka muhimmiyar ruwa game da sakamakonsu.