Kungiyar Taraiyar Turai ta nuna adawarta da hukuncin kisa akan Saddam Hussein | Labarai | DW | 05.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Taraiyar Turai ta nuna adawarta da hukuncin kisa akan Saddam Hussein

Kungiyar taraiyar turai ta yi kira ga kasar Iraqi da kada ta aiwatar da hukuncin kisa da kotu ta yanke yau a kann tsohon shugaba Saddam Hussein.

Wata sanarwa daga kasar Finland wadda take shugabancin kungiyar tace,kungiyar taraiyar turai tana adawa da hukuncin kisa akan kowane irin laifi,saboda haka bai kamata a yanke hukuncin kisan ba a wannan karo.

Kungiyar tace duk da cewa tana Allah wadai da take hakkin bil adama da kuma karya dokokin kasa da kasa da gwamnatin Saddam tayi,bai kamata a yanke wannan hukunci a kansa ba.

Yanzu haka dai kungiyoyin kare hakkin bil adama da kwarraru a fannin sharia sun ce wannan sharia da aka dauki sheakar guda a anayinta,an tabba kura kure a ciki.