Kungiyar EU ta tura wakilai zuwa Macedonia don binciken zargin da aka yiwa CIA | Labarai | DW | 27.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU ta tura wakilai zuwa Macedonia don binciken zargin da aka yiwa CIA

Wasu membobin majalisar dokokin KTT na kan hanyar zuwa Macedonia don gudanar da bincike akan zargin da wani Bajamushe yayi cewar hukumar leken asirin Amirka CIA ta yi garkuwa da shi a cikin shekara ta 2003. Khaled el-Masri ya ce bayan an kama shi a Macedonia an kai shi Afghanistan inda jami´an hukumar CIA suka yi masa tambayoyi. Wannan binciken da za´a fara yau ya zo ne kwana daya kacal bayan wani rahoto da majalisar dokokin kungiyar EU ta bayar wanda ke nuni da cewa hukumar leken asiri ta CIA ta yi amfani da filayen saukar jiragen sama a Turai wajen zirga-zirgar mutane cikin sirri har sau dubu daya tun daga shekara ta 2001.