Ko kasashe rainon Faransa na da ′yanci? | Siyasa | DW | 06.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ko kasashe rainon Faransa na da 'yanci?

Kasashen Afirka da Turawan Faransa suka yi wa mulkin mallaka sun sami 'yancin kansu shekaru 60 da suka gabata, sai dai za a iya cewa wannan 'yancin a kan takadda ne kawai.

Bildergalerie | Senegal | 60 Jahre Unabhängigkeit

Shekaru 60 da samun 'yancin kai daga Turawan Faransa a wasu kasashen Afirka

Kasashe 14 da ke yankin Kudu da Saharar Afirka ne dai suka sami 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Faransa a shekarar 1960. Wadannan kasashe kuwa sun hadar da Benin da Burkina Faso da Côte d'Ivoire da Mali da Jamhuriyar Nijar da Senegal da Togo da Kamaru da Chadi da Kwango-Brazzaville da Gabon da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Madagaska.

Sai dai ana ganin tsohuwar uwargijiyar tasu wato Faransa, na ci gaba da juya alkalarsu. Shekaru 60 bayan samun 'yancin cin gashin kan, abin tambayar shi ne: Yaushe ne Faransa za ta sakar wa kasashen Afirka da ta raina ragamar gudanar da rayuwarsu kamar yadda suke so, domin su samu damar da akwarorinsu da Turawan Ingila suka mulka ke da ita? 

DW.COM