Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Togo ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na Faransa a shekarar 1960 kuma tana cikin kasashen yammacin Afirka.
Kasar ta fuskanci juyin mulki gami da rikice-rikicen siyasa, amma zamantakewa tsakanin mutanen kasar tana cikin tsanaki.
A ranar 13 ga watan Janairu 1963 ne sojoji suka kifar da gwamnatin farko a Togo, tare da kisan shugaban kasar na wacan lokaci Sylvanus Olympio.
Kasar Cote d'Ivoire ta nuna cewa ana gab da kawo karshen takun saka da ke faruwa da kasar Mali kan kama wasu sojojin kasar 46 kimanin watanni uku da suka gabata.
Tawagar ECOWAS/CEDEAO na kan hanyar isa a Ouagadougou na Burkina Faso da zummar tattauanawa da sojijin da suka sake karbe mulki Laftanal Kanal Paul Henri Sandaogo Damiba wanda ya fice daga kasar zuwa Togo.
Hukumomin Mali na ci gaba da tsare sojojin Côte d'Ivoire 46 cikin 49 da suka kama watanni biyun da suka gabata kan zargin su da shiga Bamako ba bisa ka'ida ba.
Sojojin sun ce lamarin ya faru ne a yayin neman wasu 'yan ta'adda da suke yi a arewacin kasar, inda suka ba su ji dadin yadda bisa kuskure jirgin yakinsu ya halaka mutanen bakwai da dukkansu matasa ne ba.
A cikin shirin za a ji cibiyar sa ido ta kasa da kasa a harkokin safarar jiragen ruwa ta fidda sabon rahoto mai nuni cewar an fidda Najeriya daga jerin kasashen gabar tekun Guinea da ruwayen su ke tattare da hadduran 'yan fashin teku.
Shirin ya yi tattaki zuwa kasar Togo da kuma Tarayyar Najeriya, inda ya zakulo matasan da suka tashi tsaye domin neman abin dogaro da kansu.
Wata shahararriyar mai aikin koyar da wasannin motsa jiki a kasar Togo, ta mayar da hankali ga taimaka wa mata da ke fama da teba, da shawarwari tare da dabarun rage kiba.
Kamar koda yaushe, shirin na lalubo matasan nahiyar Afirka da suka tashi tsaye domin neman abin dogaro da kansu. A wannan kaaron, shirin ya ziyarci Najeriya da kuma kasar Togo.
Shirin na wannan mako ya ziyarci matasa a Jamhuriyar Nijar da makwabciyarta Tarayyar Najeriya, da kuma Ghana domin tattaunawa da su kan sana'o'in da suke yi domin yin dogro da kai.
Wasu masu mulki a nahiyar Afirka suna ci gaba da kaka-gida da mamaye komai tare da neman mayar da mulki siyasa zuwa gado daga iyaye zuwa 'ya'ya.
Wasu masu mulki a nahiyar Afirka na neman mayar da mulki siyasa zuwa gado daga iyaye zuwa 'ya'ya.
Tashe tashen hankula a yankin yammacin Afirka da zanga zangar adawa da mulkin soji a Sudan na daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka yi nazari.
Kasar Togo na daya daga cikin kasashen da aka rika tattara bayi daga kasashen Afirka kafin safarar su zuwa kasashen Amirka da Birtaniya da Portugal da kasashen Turai.
A cikin shirin bayan labaran duniya akwai rahoto game da halin da iyayen daliban Jangebe da aka yi garkuwa da 'ya'yansu a Zamfarar Najeriya ke ciki, sai rahoto a game da yadda rufe intanet ke kassara kasuwanci a Jamhuriyar Nijar. A Chadi kuma yajin aikin kungiyar kwadago na haifar da komabaya.
Wani atisayen hadin gwuiwa tsakanin rundunar soji da ta 'yan sanda a Ghana ya sake karbo ikon yanki Volta awowi kalilan bayan masu rajin kafa kasar Togoland suka karbe iko da yankin.