Gabon tana cikin kasashen Afirka da Faransa ta yi wa mulkin mallaka kafin samun 'yanci a shekarar 1960, tana cikin kasashe masu arzikin man fetur.
Kana tana cikin kasashen Afirka da suka tsallake juyin mulki na sojoji sannan akwai zaman lafiya tsakanin jama'ar kasar. Kasar tana da dangantaka har yanzu mai karfi da Faransa.