Kimanin ′yan gudun hijira dubu 450 sun shigo Jamus a wannan shekara | Labarai | DW | 10.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kimanin 'yan gudun hijira dubu 450 sun shigo Jamus a wannan shekara

Shugaban jam'iyyar SPD kuma ministan tattalin arzikin Jamus Sigmar Gabriel ya nuna bukatar a samar da halattattun hanyoyin shigowa Turai.

Ministan tattalin arzikin Jamus wanda har wayau shi ne shugaban jam'iyyar SPD Sigmar Gabriel ya sake yin kira da a gaggauta samar da wata manufa kan baki da ke son yin kaka-gida a Jamus. Ya ce da haka ne kawai za a yi maganin kungiyoyin da ke fataucin dan Adam. Ya ce ba za a iya haramta yin kaura ba, saboda haka ya zama wajibi a bude halattattun hanyoyin shigowa Turai. Bisa kalamansa dai a bana 'yan gudun hijira kimanin dubu 450 suka shigo tarayyar Jamus. A lokaci daya kuma mataimakin shugabar gwamnatin Jamus din ya soki lamirin wasu kasashen kungiyar EU da nuna son kai, inda suke kin karbar 'yan gudun hijira.