Khamenei ya amince da yarjejeniyar nukiliya | Labarai | DW | 21.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Khamenei ya amince da yarjejeniyar nukiliya

Shugaban juyin-juya halin Musulunci na kasar Iran Ayatollah Seyed Ali Khamenei ya mara baya ga yarjejeniyar da aka cimma kan batun nukiliyar Iran din.

Ayatollah Seyed Ali Khamenei jagoran addinin Islama a Iran

Ayatollah Seyed Ali Khamenei jagoran addinin Islama a Iran

Ayatollah Khamenei wanda shi ne jagoran koli da ke yanke hukunci na karshe kan al'amuran da suka shafi kasar, ya bayyana mara bayan nasa kan yarjejeniyar nukiliyar ta kasar ta cimma da kasashe shida masu karfin fada aji a duniya ne cikin wata takarda da ya aikewa Shugaba Hassan Rouhani na kasar wanda ke zaman mai sassaucin ra'ayi, wadda kuma aka karanta a gidan talabijin din kasar.

Sai dai jagoran juyin-juya halin ya gargadi gwamnatin kasar ta Iran da ta yi aiki da tanade-tanden yarjejeniyar cikin sanya idanu da lura saboda a cewarsa Amirka ba abar yadda bace a gare su. Cikin watan Yulin da ya gabata ne dai kasar ta Iran ta cimma yarjejeniya kan shirinta na makamashin nukiliya da aka dade ana ta takaddama a kansa tare da kasahen Amirka da Faransa da Birtaniya da Rasha da China da kuma Jamus.

A karkashin yarjejeniyar dai Iran za ta dakile shirin nukiliyarta yayin da su kuma za su dage mata takunkumin karya tatalin arzikin da suka kakaba mata bisa zarginta da yunkurin mallakar makaman kare dangi, zargin da ta ke ci gaba da musanta shi tana mai cewa shirinta na zaman lafiya ne.