1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta goyi bayan Czech wajen samar wa Ukraine makamai

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 6, 2024

Sauran kasashen da suka alkawarta bayar da na su tallafin sun hada da Faransa da Netherlands da Belgium, sai Canada da Denmark da kuma Lithuania

https://p.dw.com/p/4dEv8
Hoto: William Noah Glucroft/DW

Jamus ta goyi bayan yunkurin Jamhuriyar Czech na samar wa Ukraine karin makamai don ci gaba da kare kanta daga mamayar da Rasha ta yi mata yau sama da shekaru biyu.

Karin bayani:Zelensky zai halarci taron tsaro na Jamus

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Steffen Hebestreit, ya ce Berlin ta jima tana doguwar tattaunawa da Prague don samun karin goyon bayan tallafa wa Ukraine da makamai.

Karin bayani:Ministatar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta yi watsi da batun sulhu da Putin kan Ukraine

Shugaban Jamhuriyar Czech Petr Pavel, wanda kuma ya taba rike mukamin sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO, ya ce taron tsaro da aka gudanar a tsakiyar watan Fabrairun da ya gabata a birnin Munich ya samar da haske matuka kan wannan shiri.

Sauran kasashen da suka alkawarta bayar da na su tallafin sun hada da Faransa da Netherlands da Belgium, sai Canada da Denmark da kuma Lithuania.